Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Haɗaɗɗiyar ƙungiyar ’Yan Kasuwa ta Jihar Kano (AMATA) ta bayyana ƙorafi kan cewa ba a ba ta wakilci a ƙunshin kwamitin da Gwamnatin Jihar Kano ta kafa domin duba batun gobarar da ta auku a Kasuwar Singa.
ƙungiyar ta kuma gudanar da taron saukar Alƙur’ani da addu’o’i na musamman domin neman kariya ga jihar da kasuwanninta, sakamakon yawaitar gobara, musamman wadda ta auku a Kasuwar Singa.
Shugaban AMATA na jihar, Alhaji Abdul’Aziz ɗalha Musa, ya bayyana cewa an shirya addu’o’in ne domin neman yafiya da kariyar Allah kan iftila’in gobarar da ta jawo asarar dukiya mai yawa ga ’yan kasuwa. Ya ce a wajen taron an sauke Alƙur’ani sau goma, tare da gudanar da zikiri da addu’o’i na musamman.
Dangane da gobarar Kasuwar Singa, Musa ya ce sun gamsu da yadda aka tantance ’yan kasuwar da abin ya shafa sama da 1,500, tare da haɗin gwiwar hukumomin NEMA da SEMA.
Ya ƙara da cewa suna sa ran tallafin da Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Kano suka yi alƙawari zai isa ga waɗanda gobarar ta shafa domin rage musu raɗaɗin da suka fuskanta.
Sai dai shugaban na AMATA ya nuna damuwa kan rashin wakilcin ƙungiyar a kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa ƙarƙashin jagorancin Sakataren Gwamnati domin duba batun tallafin, duk da cewa a ofishin ƙungiyar ne aka gudanar da aikin tantancewar ’yan kasuwar da abin ya shafa.
Ya ce sun rubuta takarda ga Sakataren Gwamnati da kuma Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar domin a sake duba lamarin, yana mai bayyana zaton cewa mai yiwuwa Gwamnan Kano ba shi da masaniya kan yadda aka tsara kwamitin.
Musa ya roƙi Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, da ya sake duba tsarin kwamitin domin tabbatar da adalci da kuma wakilcin da ya dace, yana mai jaddada cewa manufarsu ita ce rage raɗaɗin da ’yan kasuwa ke ciki bayan iftila’in gobarar.
A nasa ɓangaren, Sarkin Kasuwar Singa, Alhaji Isah Abba, ya bayyana cewa addu’a ita ce mafita ga duk wani iftila’i, yana mai kira ga al’umma da su ƙara komawa ga Allah domin samun zaman lafiya da kariya.
