NNPP ta bayyana dalilin ƙaurace wa zaɓen cika gurbi a Kano bayan ƙarancin fitowar masu kaɗa ƙuri’a

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Jam’iyyar APC ta lashe zaɓuka a ƙananan hukumomin Ungogo da Kano Municipal a Kano bayan da jam’iyyar adawa ta NNPP ta ƙi shiga zaɓen.

Zaɓen cike gurbin dai an yi ne a ranar Asabar biyo bayan rasuwar ‘yan majalisa biyu a Kano a watan Disamba, Aminu Sa’adu (Ungogo) da Sarki Aliyu (Kano Municipal). Dukkan mutane biyun ‘yan jam’iyyar NNPP wadda a lokacin ita ce ke mulki kafin sauyin sheƙar gwamna Abba Yusuf zuwa zuwa APC a watan da ya gabata.

‘Ya’yan ‘yan majalisar da suka rasu – Aminu Sa’adu Jr. da Nabil Daneji – su ne suka maye gurbin kujerun iyayensu a APC. Kuma dukkan jam’iyyun NNPP da APC sun ayyana sunayen ‘yan takarar ne sai dai sun zaɓi shiga jam’iyyar APC.

Daneji ya samu ƙuri’u 7,484 inda ya zama ɗan majalisar Kano Municipal bayan ayyana nasararsa da jami’in zaɓe, Ibrahim Siraj, ya yi.

Haka kuma a mazaɓar Ungogo, ɗan takarar APC, Sa’ad, ne ya lashe zaɓe da ƙuri’u 8,975 bayan jami’in zaɓe, Ali Abdullahi, ya ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Manhaja ta rawaito yadda aka samu ƙarancin masu fitowa kaɗa ƙuri’a a dukkan ƙananan hukumomin.

Babban jami’in hukumar zaɓe (REC) ta INEC) a Kano, Abdu Zango, ya alaƙanta rashin fitowar al’umma a lokacin zaɓen da rashin shigar jam’iyyun siyasa.

A yayin da yake magana da manema labarai a lokacin da yake duba halin da ake ciki, Zango ya bayyana zaɓen da cewa an shi cikin kwanciyar hankali duk da akwai ƙarancin masu kaɗa ƙuri’a a wasu akwatunan.

“Tun da fari, ina tunanin sa zaɓen a lokacin azumi ya karya guiwa. Na biyu, ina tunanin zaɓen ƙarami ne sosai da ya shafi ‘yan takara biyu kawai ga kuma ba jam’iyyu da yawa. Ina ga jam’iyyu 9 ne suka shiga zaɓe,” inji Zango.

Sai dai bayan komawar gwamnan Kano APC, sai su ‘ya’yan suka zaɓi su mara wa gwamna baya da zaɓar yin takara a ƙarƙashin jam’iyyar APC.

Mai magana da yawun Kwankwasiyya Habibu Mailemu, ya bayyana a cikin wani jawabi cewa NNPP ta zaɓi ƙin sauya sunayen da ta bayar tun farko ne bayan sun koma APC.

Wannan mataki ya biyo umarnin Kwankwaso wanda ya ce ya kamata a taimaka wa yaran domin su samu kujerar majalisa ba tare da la’akari da jam’iyyar da za su ba.

Mailemu ya ce, “matakin Kwankwaso na ƙin maye gurbin ‘yan takara na da alaƙa da irin tausayawa da goyon baya da mutuntawa a maimakon siyasa.”

“Duk da wannan abu da ya faru na sauya sheƙar ‘yan takarar zuwa APC, jagoranmu ya nuna dattako da mutunta iyalan waɗanda suka rasu saboda irin sadaukarwa da suka yi wa tafiyar Kwankwasiyya. Wannan ta sa ya mutunta matakin da ya ɗauka tun da farko.”

“Ya ce a bar ‘ya’yan ‘yan majalisar da suka rasu su shiga majalisar dokoki ba tare da la’akari da jam’iyyarsu ba. Wannan mataki cike yake da ƙauna da tausayawa.”

“Don haka, NNPP tana sane ta ƙi maye sunayen ‘yan takarar da wasu duk da cewa sun fice daga jam’iyyar. Wannan mataki ya nuna ƙarara irin tsarin da muke da shi a NNPP.”

“Wannan dalili ne ya sa babu sunan jam’iyyar NNPP a kan takardar zaɓe saɓanin labaran ƙanzon kurege da ake yaɗawa,” ya faɗa.

By ukarofi