Iran ta tabbatar da rasuwar Jagoran Musuluncin ƙasar a harin Amurka da Isra’ila

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Iran da kafar yaɗa labaran ƙasar sun tabbatar da mutuwar Jagoran Musuluncin ƙasar, Ali Khamenei bayan ruwan wuta da Amurka da Isra’ila suak ƙaddamar a ranar Asabar, lamarin da ya yi sanadin faɗaɗa rikici a yankin Gabas ta Tsakiya da sanya alamar tambaya game da makomar ƙasar.

Hakan na zuwa ne jim-kaɗan bayan ikirarin farko da shugaba Donald Trump ya yi na kisan jagoran addinin a hare-haren da suka kai a sassan ƙasar.

A sanarwar kafar yada labaran, ba a bayyana yadda aka kashe jagoran addinin, mai shekaru 86 ba da kuma wanda zai gaje shi tun bayan da ya fara mulkin ƙasar a shekara 1989.

Majalisar Ƙoli ta tsaron Iran ce ta tabbatar da mutuwar Khamenei tana mai zargin Amurka da Isra’ila, kamar yadda sanarwar ta fitar.

Sanarwar ta ce shahadar Khamenei za ta kasance mafarin “yaki da azzalumai”.

Ta kara da cewa an kashe Ayatollah Khamenei ne da safiyar Asabar a ofishinsa. Haka kuma, harin ya yi sanadiyyar mutuwar ‘yarsa surikinsa da jikansa.

A cewar kamfanin dillacin labarai na Fars da ke kusanci da dakarun juyin juya hali na Iran, akwai rahotannin da ke cewa akwai surukar Khamenei cikin waɗanda aka kashe.

Kafar talabijin ta Iran ta bayar da sanarwar kwanaki 40 na zaman makoki a Iran da kwana bakwai na hutu domin jimamin mutuwar jagoran.

By Babaji