Siyasa

Burina na sauke nauyin al’ummar da nake shugabanta – Hon. Baba-Goni

Burina na sauke nauyin al’ummar da nake shugabanta – Hon. Baba-Goni

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Ƙaramar Hukumar Fune a Jihar Yobe, Hon. Baba-Goni Mustapha Bade ya ce babban burinsa shi ne ya sauke nauyin al'ummar da yake shugabanta, bayan da ya bayyana irin romon dimukradiyyar da ya samar tun bayan hawansa kujerar mulki a qaramar hukumar, inda ya bayyana cewa dukkan nasarorin sun samu ne bisa kyakkyawan jagorancin na Gwamna Mai Mala Buni. Hon. Baba-Goni ya ce babban burinsa shi ne ya ga ya sauke nauyin da al'ummarsa suka dora mishi, ta hanyar ayyukan raya karamar hukumar da inganta rayuwar matasa, tsofaffi, yara da manya. Ya ce shi…
Read More
Kotun Ƙoli ta tabbatar da nasarar Gwamnan Sakkwato

Kotun Ƙoli ta tabbatar da nasarar Gwamnan Sakkwato

Kotun Koli ta tabbatar da nasarar zaben Gwamna Aliyu Ahmad din ne a zaman da ta yi ranar Alhamis inda ta yi watsi da karar da Jam’iyyar PDP da dan takararta na gwamna Saidu Umar suka shigar na kalubalantar nasarar zaben da Aliyu ya samu a zaben 2023. A hukuncin kotun, wanda Mai shari’a Tijani Abubakar ya karanta, ya yi watsi da karar da Jam’iyyar PDP da dan takararta na gwamna Saidu Umar suka shigar na kalubalantar nasarar zaben Gwamna Ahmed Aliyu. Kwamitin alkalin ya tabbatar da hukuncin da kotun daukaka kara da ke Abuja ta yanke na cewa PDP…
Read More
Kotun Ƙoli ta ayyana Fubara a matsayin zaɓaɓɓen Gwamnan Ribas

Kotun Ƙoli ta ayyana Fubara a matsayin zaɓaɓɓen Gwamnan Ribas

Daga BASHIR ISAH Kotun Koli da ke zamanta a Abuja ta ayyana Sim Fubara a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamna a Jihar Ribas. Kotun ta yanke hukuncin haka ne a zaman da ta yi a ranar Alhamis bayan da ta karbi bayana daga bangarorin da shari’ar ta shafa. an takarar gwamnan na Jama’iyyar APC a jihar a zaben 2023 da ya gudana, shi ne ya daukaka kara inda ya kalubalanci nasarar da Gwamna Fubara ya samu a zaben. Nasarar Fubara  a Kotun Kolin na zuwa ne a daidai lokacin da ruwa ke ci gaba da tsami a tsakaninsa da…
Read More
Ɗan APC da ɗan PDP Ɗanjuma da Ɗanjummai ne – Sule Lamiɗo

Ɗan APC da ɗan PDP Ɗanjuma da Ɗanjummai ne – Sule Lamiɗo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon gwamnan jihar Jigawa, kuma jigo a Jam'iyyar PDP ya ce zargin da tsohon shugaban rikon kwarya na jam'iyyar APC Chief Bisi Akande ya yi cewa idan PDP ta dawo mulki 'yan Nijeriya za su sake shiga qunci ba gaskiya ba ne. Alhaji Sule Lamido ya ce duk dan APCn da yake ganin PDP ce ta lalata Nijeriya to da shi a ciki, kasancewar shi ma asali dan PDP ne. Sule Lamido ya ce ya yi mamakin kalaman Bisi Akande kan cewa PDP musiba ce, annobar bala'i ce azaba ce, amma duk da hakan…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta keɓe yanke hukunci kan zaɓen gwamnan Sakkwato

Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta keɓe yanke hukunci kan zaɓen gwamnan Sakkwato

Kotun Koli da ke Abuja, ta kebe yanke hukunci kan karar da jam'iyyar PDP da dan takararta, Saidu Umar, suka daukaka na kalubalantar nasarar da Gwamna Ahmad Aliyu ya samu a matsayin zababben gwamnan jihar a zaben 2023. Kwamitin akalai biyar karkashin jagorancin Mai Shari'a Kudirat Kekere-Ekun, ya dauki wannan mataki ne yayin zaman shsari'ar da ya yi a ranar Laraba. Kotun ta dage yanke hukunci kan shari'ar ne zuwa wani lokaci wanda ba ta ayyana ba. Kuma ta yi hakan ne bayan da ta karbi bayanai daga lauyoyin bangarorin da shari'ar ta shafa.
Read More
Kotun Ƙoli: Zamfarawa sun yi fitar farin dango don taya Gwamna Lawal murna

Kotun Ƙoli: Zamfarawa sun yi fitar farin dango don taya Gwamna Lawal murna

Daga BASHIR ISAH A ranar Litinin da ta gabata dubban Zamfarawa cike murna suka yi dandazo a Gusau, babban birnin jihar domin tarbar Gwamna Dauda Lawal in Gusau, bayan dawowa daga Kotun Ƙoli. A ranar Juma'ar da ta gabata Kotun Ƙoli mai zamanta a Abuja ta tabbatar  da Gwamna Lawal a matsayin wanda ya lashe zabe Gwamnan Zamfara, tare da yin watsi da karar da bangare hamayya ya daukaka na kalubalantar nasarar tasa. Cikin sanarwar manema labarai da ya fitar, Kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya ce masoyan gwamnan sun yi fitar farin dango don nuna farin cikinsu dangane da…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta keɓe yanke hukunci kan shari’ar zaɓen gwamnan Kebbi

Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta keɓe yanke hukunci kan shari’ar zaɓen gwamnan Kebbi

Kotun Ƙoli ta keɓe yanke hukunci kan karar da aka dauka ta neman a sauke Dr Nasir Idris na jam'iyyar APC a matsayin Gwamnan Jihar Kebbi. Kotun ta dauki wannan matsaya yayin zaman ci gaba da sauraren shari'ar da ta yi ranar Talata karkashin jagorancin Mai Shari'a Kudirat Kekere-Ekun, bayan ta karrbi bayanan lauyoyin duka bangarorin. Kotun ta ce za ta sanar da bangarorin da lamarin ya shafa baya ta tsayar da lokacin da za ta yanke hukunci kan shari'ar. Jam'iyyar PDP a Jihar Kebbi da dan takarar gwamnanta a zaben 2023, Manjo Janar Aminu Bande, su ne suka daukaka…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta keɓe yanke hukunci kan shari’ar zaɓen gwamnan Nasarawa

Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta keɓe yanke hukunci kan shari’ar zaɓen gwamnan Nasarawa

Kotun Ƙoli ta keɓe yanke hukunci kan shari'ar zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa da ke gabanta. Kotu ta yi hakan ne a zaman ci gaba da sharilar da ta yi a wannan talatar. Ta ce za ta sanar da bangarorin da shari'ar ta shafa ranar da za raba gardama idan ta tsayar da rana nan gaba. Ana fafata shari'ar ne tsakanin Gwannan jihar, Injiniya Abdullahi Sule da kuma Jam'iyyar PDP a jihar tare da dan takararta na gwamna, David Ombugadu
Read More
Buni ya samar da romon dimukraɗiyya a Nengere – Hon. Yerima

Buni ya samar da romon dimukraɗiyya a Nengere – Hon. Yerima

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Karamar Hukumar Nengere a Jihar Yobe, Hon. Salisu Yerima ya bayyana irin kokarin da Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya yi wajen samar da romon dimukradiyya ga al'ummar yankin tun bayan hawansa mulkin jihar a 2019. Hon. Yerima ya ce Gwamna Buni ya yi abin a yaba da irin jagorancinsa na cire kyashi wajen dorawa daga inda tsohon gwamnan jihar, kuma Ministan Harkokin 'Yan Sanda na yanzu, Sanata Ibrahim Geidam ya tsaya. Ya ce an samu nasarori masu tarin yawa da suka haifar wa jihar da mai ido, inda ya ce shirye-shiryen…
Read More