An yaba wa Gwamna Zulum kan gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi cikin lumana a Jihar Borno

Spread the love

Daga GAMBO ISA a Abuja

Shugaban ƙaramar Hukumar Kaga a Jihar Borno, Hon. Mairu Goni Abdullahi, ya bayyana jin daɗinsa tare da yaba wa Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, bisa nasarar da aka samu wajen gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar cikin kwanciyar hankali, tsari da adalci. Ya ce wannan zaɓe ya nuna ƙwazon gwamnati da jajircewarta wajen ƙarfafa dimokiraɗiyya a matakin ƙasa.

Hon. Mairu Goni Abdullahi ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manema labarai a hedkwatar ƙaramar Hukumar Kaga, inda ya jaddada cewa zaɓen ya gudana lafiya ba tare da matsalolin tsaro ba. A cewarsa, wannan nasara ta samo asali ne daga tsare-tsare da kyakkyawan shugabanci da Gwamna Zulum ya shimfiɗa tun farko domin tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan al’umma.

Shugaban ƙaramar hukumar ya ƙara da cewa, gwamnatin Farfesa Zulum ta nuna gagarumin jajircewa wajen sake gina Jihar Borno bayan ƙalubalen tsaro da ta fuskanta a shekarun baya. Ya ce ƙoƙarin gwamnan wajen dawo da zaman lafiya ya samar da damar aiwatar da manyan ayyukan raya ƙasa a sassa daban-daban na jihar.

Hon. Mairu Goni Abdullahi ya yaba wa gwamnan musamman kan gina da gyaran manyan tituna da na cikin birane da karkara, wanda ya ce hakan ya taimaka matuƙa wajen sauƙaƙa zirga-zirga da bunƙasa harkokin kasuwanci a faɗin jihar. Ya ce titinan sun haɗa al’umma tare da buɗe ƙofofi ga cigaban tattalin arziki.

Haka kuma, ya jinjinawa Gwamna Zulum bisa gina asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya tare da inganta kayan aiki da walwalar ma’aikatan lafiya. A cewarsa, waɗannan matakai sun taimaka wajen rage mutuwar mata masu juna biyu da jarirai, tare da inganta lafiyar al’ummar jihar gaba ɗaya.

A fannin ilimi kuwa, Hon. Mairu Goni Abdullahi ya bayyana cewa gwamnatin Zulum ta yi fice wajen gina makarantu, gyara tsofaffi da kuma samar da kayan karatu da horar da malamai. Ya ce wannan ƙoƙari ya taimaka wajen dawo da yara makaranta, musamman a yankunan da rikici ya shafa a baya.

A ƙarshe, Shugaban ƙaramar Hukumar Kaga ya tabbatar wa Gwamna Babagana Umara Zulum da cikakken goyon bayan shugabannin ƙananan hukumomi da al’ummar Kaga baki ɗaya. Ya ce za su ci gaba da haɗa kai da gwamnatin jihar domin tabbatar da ɗorewar zaman lafiya, cigaban rayuwar al’umma da kuma tabbatar da cewa dimokiraɗiyya ta yi ƙarfi a Jihar Borno.

By ukarofi