An rantsar da ɗaliban Jami’ar Bayero da suka samu shaidar ƙwarewa akan sanin magunguna

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

An rantsar da ɗalibai da suka kammala karatun digiri na farko a tsangayar harhaɗa magunguna na Jami’ar Bayero da basu shaidar zama ƙwararrun masu harhaɗa magunguna na ƙasa.

Taron shan  rantsuwar da bada shaidar ya gudana ne a ɗakin taro na harabar tsohuwar jami’ar da ya samu halartar mutane da dama da suka haɗa da  shugabannin sassa na jami’ar da malamai da iyaye da sauran mamyan baki.

Da yake ƙarin haske game da taron Dakta Bashir Cheɗi ya ce taron rantsuwar shine karo na uku na baiwa ɗalibai da suka yi digirin farko na samun shaidar ƙwarewa na ƙasa a sanin magunguna,  rantsar da su da aka yi zai ba su dama su iya neman aiki a matsayin ƙwararru akan sanin magunguna.

Ya ce ɗaliban a shakara 2023 ya kamata su kammala karatu amma saboda a tsarin kalandar koyarwa ta jami’a ta sha bamban da ta girigori wata shekarar na shiga wata, amma waɗanda aka rantsar aka ba shaidar ya kamata a ce tun a zango na 2023/24 suka gama.

Ya yi nuni da cewa kwas ɗin na tsawcn shekaru shida ne sai ya kasance a 2020 an samu annobar kuroma aka rufe ƙasa watanni ba a karatu a zaman nan sun yi asarar shekara guda bayan an gama kurona aka kuma  tafi yajin aiki na malamam jami’a wajen wata takwas, kusan zango guda shi yasa za a ga 23/24 ba don Koroma ba da da yajin aiki da 2024 ya kamata su yi amma saboda wannan shekara biyun sai a 2026 aka yi.

Dakta Bashir Cheɗi ya ce akwai rantsuwa ta kama aiki da ɗalibai suka ɗauka da mutum yake rantsuwa tsakaninsa da Allah kowa zai yi aikinsa bisa adalci da tausayi da sanin ya kamata da rashin nuna bambanci na addini da na ƙabila ko wani abu.

Ya yi jan hankali ga waɗanda suka ɗau rantsuwar su tuna rantsuwa suka yi tsakanin su da Allah duk inda mutum ya sami kansa ya tuna da rantsuwar da ya yi  aiki da gaskiya zai gama lafiya da yardar Allah.

Ya ce yanzu a ƙasarnan adadin ƙwararru akan magunguna basu kai yanda yakamata ba a cikin al’umma, domin hukumar lafiya ta duniya ta nuna ana son a duk mutun 500 aƙalla ace akwai kwararren masanin magunguna ɗaya amna a ƙasar nan adadin yana tafiya wajen ƙwararren masanin magunguna ɗaya zuwa wajen mutum 100,000 ma.

Dakta Bashir Chadi ya ce wannan na nuna har yanzu a ƙasar nan ana da buƙatar ƙarin masana a harkar magunguna.Kuma abinda yake kawo samun magunguna na jabu rashin ƙwararru wadatattun masana magunguna ne  shi ya da dama kowa ma yanzu sai ya shiga harkar  da akwai ƙwararru masana wannan matsala za ta kau.

Ya ce yanzu abinda yake faruwa kowa saboda rashin wadatattun ƙwararru kowa so yake ya shiga harkar wanda ya san harkar da wanda bai sani ba kawai gani ake harka ce ta samun kuɗi wanda ya sani da wanda bai sani ba kawai ya ya  zani na je na sayo, ba zai iya tantance ingantacce ne ko ba ingantacce bane.

Dakta Bashir Cheɗi ya ce amma da irin waɗannan yara ɗalibai da suka yaye  suka sha rantsuwa akwai  fatan na gaba ma waɗanda  za a yaye za su rage wannan matsalolin dan za a sami masana kwararru da suka san meye magani suka san yanda za su bambance in suka gani wannan ingatacce ne  wannan ba mai inganci bane wannan zai sa waɗanda suke yan taka haye su ragu wannan zai kawo sauƙin matsaloli.

By ukarofi