Jami’ar Bayero ta yaba wa Hukumar Hadejia Jama’are kan kammala ayyukan samar da ruwa

Spread the love

Daga WAKILINMU 

Hukumar Gudanarwar Jami’ar Bayero Kano, ranar 12 ga watan Janairu 2026 sun kai ziyayar sada zumunci da godiya a Hukumar Raya Kogunan Haɗejia da Jama’are don nuna jin daɗi da godiya kan kammala ayyukan samar da ruwa a sassan jami’ar daban-daban masu muhimmancin gaske.

Shugaban Jami’ar Bayero Farfesa Haruna Musa, ne ya jagoranci tawagar zuwa Hukumar Raya Kogunan Hadejia da Jama’are domin bayyana jinjina da godiya kan kammala ayyukan samar da ruwa da aka kwashi tsawon lokaci jami’ar ke fama da rashin ruwa. 

Yace ayyukan da aka fara tsakanin watan Disamba a shekarar 2025 zuwa watan Janairu 2026 ya taimaka kwarai wajen samar da isashen ruwa ga ɗalibai da ma’aikata da al’ummar dake harkokin yau da kullum a sassa daban-daban na jami’ar.

Farfesa Haruna Musa ya bayyana cewa cikin ayyukan da aka kammala sun haɗa da samar da famfunan ruwa masu amfani da solar da gyaran tankunan adana ruwa na ƙarƙashin ƙasa da gyara hanyoyin ruwa dake kai ruwa ɗakunan kwanan ɗalibai a sabuwar jami’ar da tsohuwar jam’iar da Goron Dutse da Asibitin Malam Aminu Kano duk dake ƙarƙashin Jami’ar Bayero.

Yayin jawabin Shugaban Hukumar Raya Kogunan Hadejia da Jama’are Engr. Rabiu Suleiman Bichi ya bayyana jin daɗin da ziyarar da Hukumar Jami’ar Bayero suka kawo wa hukumarsa. 

Ya ce hakan zai ƙarfafa musu gwiwa wajen ƙoƙarin cigaba da ayyukan cigaba da hukumar ke yi. Ya ce aikin hukumar ne kula da bunƙasa da sarrafa ruwa a jihohin Kano da Jigawa da Bauchi domin amfani da shi a gidaje da masana’antu da ayyukan noma inda ya ce Jami’ar Bayero na cikin jihohin da hukumar ke da ikon gudanar da ayyukanta.

Engr. Bichi ya ƙara da cewa tallafawa jami’ar da ruwa na da muhimmanci saboda kacencewar ta cibiyar bada ilimi da bincike a wannan yankin.

Hon. (Dr) Musa Iliyasu Kwankwaso Daraktan Kuɗi da Gudanarwa na Hukumar Raya Kogunan Haɗejia da Jama’are da Manyan Daraktocin Hukumar ne suka tarbi manyan baƙi da suka kawo ziyayar daga Jami’ar Bayero.

By ukarofi