Daga RABIU SANUSI a Kano
Wata Babbar Kotu a Jihar Kano ta soke matakin rushe shugabannin jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP) a matakan jiha, kananan hukumomi da mazabu, tare da bayyana hukuncin Kwamitin Gudanarwa na ƙasa (NWC) a matsayin babu inganci a doka.
Mai shari’a Nasiru Saminu ne ya bayar da umarnin eɗ-parte a ranar Talata, inda ya kuma hana Kwamitin Gudanarwa na ƙasa na NNPP ɗaukar duk wani sabon mataki da ya shafi tsarin shugabancin jam’iyyar a Kano, har zuwa lokacin sauraron da yanke hukunci kan Motion on Notice da masu ƙara suka shigar.
ƙarar mai lamba K/06/2026, wadda Abdullahi Zubairu Imam da wasu mutum biyar suka shigar a madadin kwamitin zartarwa na NNPP a kananan hukumomi 44 na jihar Kano, an shigar da ita ne a kan jam’iyyar NNPP, domin ƙalubalantar matakin rushe shugabannin.
A cikin umarnin wucin-gadi, Mai shari’a Saminu ya umurci dukkan ɓangarorin da su ci gaba da bin halin da ake ciki (status ƙuo ante) tun daga ranar 30 ga Disamba, 2025, kafin umarnin rushe shugabannin da NWC ta fitar.
A cewar umarnin kotun, bayan sauraron roƙon da lauyoyi K.K. Njidda da S.A. Muhammad suka gabatar a madadin masu ƙara, kotun ta bayar da umarnin hana jam’iyyar NNPP, wakilanta, jami’anta ko duk wata ƙungiya da ke aiki a madadinta daga naɗa kwamitocin rikon kwarya a matakan jiha, ƙananan hukumomi da mazaɓu a Kano ko ɗaukar duk wani mataki da ya shafi batun da ake shari’a a kai har sai an yanke hukunci na ƙarshe.
Haka kuma, kotun ta amince wa masu ƙara da su yi wa jam’iyyar hidimar takardun shari’ar a Sakatariyar ƙasa ta NNPP da ke lamba 11, Titin Mahatma Gandhi, Area 11, Garki, Abuja, duk da kasancewar wajen yana waje da ikon kotun.
Abin tunawa shi ne, Kwamitin Gudanarwa na ƙasa na NNPP ya sanar da rushe shugabannin jam’iyyar a dukkan matakai a jihar Kano, bayan dakatar da Hon. Hashim Dungurawa daga muƙamin shugaban jam’iyyar a jihar.
Daga bisani, an naɗa Abdullahi Abiya a matsayin shugaban riƙon ƙwarya, matakin da yanzu kotu ta sake tabbatar da sahihancinsa har zuwa ci gaba da shari’ar.
