Kiraye-kirayen cewa na ajiye takara cin amanar ‘yan Nijeriya ne – Atiku

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Tsohon Mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi gargaɗi kan kiraye-kirayen da ake yi masa na ya ajiye takara a yaƙin neman shugabancin ƙasa ƙarƙashin jam’iyyar haɗaka ta ADC, yana mai cewa hakan cin amanar ‘yan Nijeriya ne.

Sanarwar da mai bai wa Atiku shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, ya fitar ta bayyana cewa duk wani yunƙuri na ganin Atiku ya ajiye takara zai goyi bayan manufofin kama-karya ne kawai tare kuma da tauye haƙƙin dimokuraɗiyya a Nijeriya.

Sanarwar ta ce a cikin shekaru kusan uku da suka gabata, ‘yan Nijeriya sun fuskanci wahalhalu masu tsanani sakamakon manufofin tattalin arziƙi a ƙarƙashin mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Sanarwar ta kuma zargi gwamnatin Tinubu da ƙoƙarin mayar da siyasar Nijeriya ta zama ƙarƙashin jam’iyya ɗaya ta hanyar raunana jam’iyyun adawa.

Sanarwar ta ƙara da cewa “Jam’iyyar ADC za ta ci gaba da gudanar da tsarin tsayar da ɗan takararta kuma duk wani matsin lamba daga APC ko masu tsoma baki daga waje ba zai yi tasiri ba saboda ba su da ikon yin zagon ƙasa kan wanda ADC za ta tsayar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa.

By ukarofi