Siyasa

Yahaya Bello ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Sanata a Kogi ta tsakiya

Yahaya Bello ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Sanata a Kogi ta tsakiya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Sanatan Kogi ta tsakiya a zaɓen 2027 mai zuwa. Bello ya bayyana hakan ne a wata ziyara da ya kai fadar Ohinoyi na Ebiraland, inda ya gana da sarakunan gargajiya, malaman addini da masu ruwa da tsaki na yankin majalisar dattawa. An yaɗa bidiyon ziyarar da kuma bayaninsa a shafin Facebook mai tabbatar da Bello a ranar Litinin. "Na yarda in tsaya takarar majalisar dattawa a 2027," inji tsohon gwamnan yayin da yake jawabi a wurin taron. Gwamnan jihar Kogi, Ahmed Usman…
Read More
NNPP ta sake zaɓen Ajuji Ahmed a matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa 

NNPP ta sake zaɓen Ajuji Ahmed a matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Jam’iyyar NNPP ta sake zaɓen Ajuji Ahmed a matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa. An sake zaɓen Ahmed ne a ranar Asabar a babban taron jam’iyyar na ƙasa da aka gudanar a Abuja, inda zai yi wa’adin shekaru huɗu karo na biyu. NNPP ta kuma sake zaɓen sauran mambobin kwamitin gudanarwa na kasa, ciki har da Abba Kawu, mataimakin shugaban jam'iyyar na arewa; Onu Nwaze, mataimakin shugaban jam'iyyar na kudu; Dipo Olayokun, sakataren ƙasa; da Oladipo Johnson, sakataren yaɗa labarai na jam'iyyar. Sauran sun haɗa da Ibrahim Muhammad, mataimakin sakataren ƙasa; Bala Mohammed, sakataren tsare-tsare…
Read More
Yaƙi da cin hanci ba lamari ne na siyasa ba — Fadar Shugaban ƙasa

Yaƙi da cin hanci ba lamari ne na siyasa ba — Fadar Shugaban ƙasa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Fadar Shugaban ƙasa ta yi watsi da zargin da wasu ‘yan adawa suka yi cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na amfani da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) a matsayin makamin siyasa, tana mai cewa hukumar mai zaman kanta ce da ke aiki bisa tanadin doka. A cikin wata sanarwa da Mai Ba Shugaban ƙasa Shawara ta Musamman kan labarai, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Lahadi, fadar ta ce shugaba ƙasa ba ya bayar da umarni ga kowace hukumar yaƙi da cin hanci kan wanda za a bincika ko a gurfanar.…
Read More
Kungiyar ’yan takarar ADC ta Kano ta gudanar da taron tattaunawa kan cigaban tafiyarsu

Kungiyar ’yan takarar ADC ta Kano ta gudanar da taron tattaunawa kan cigaban tafiyarsu

Daga RABIU SANUSI a Kano Kungiyar ’yan takarar Jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) ta Kasa reshen Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Hon. Haruna Yahaya Kadana ta gudanar da taron tattaunawa domin duba matsayin jam’iyyar cigaban da aka samu da kuma kalubalen da ke gabansu yayin shirye-shiryen zaɓen da ke tafe. A jawabinsa yayin taron Shugaban ƙungiyar Hon. Kadana ya bayyana irin ƙoƙarin da jam’iyyar ke yi wajen ƙarfafa tsarin ta da tabbatar da cewa tafiyar siyasar ADC ta samu gagarumin ci gaba a Kano. Ya ce jam’iyyar na ƙara samun karɓuwa a wuraren al’umma daban–daban. Ya kuma bayyana cewa kwanan nan…
Read More
Gwamna Adeleke ya koma Jam’iyyar Accord, yayin da Fubara ya koma APC

Gwamna Adeleke ya koma Jam’iyyar Accord, yayin da Fubara ya koma APC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Osun Ademola Adeleke ya bayyana komawarsa Jam'iyyar Accord, inda ya ce a cikinta ne zai yi takarar neman wa'adin mulkinsa na biyu a zaɓen da za a yi a shekarar 2026. Gwamnan ya bayyana haka ne a wani taro da ya gudana a fadar gidan gwamnatin jihar, inda ya yi maraba da jagororin jam'iyyar na jiha da na ƙasa. "Tun a ranar 6 ga watan Nuwamba na yanke shawarar komawa Jam'iyyar Accord domin in yi takarar tazarce bayan tattaunawa da na yi da masu ruwa da tsaki da mazauna jiharmu ta Osun."…
Read More
Ba za a taɓa haɗa gwamnatin Abba da ta baya ba wajen gudanar da ayyukan cigaba a Jihar Kano – Bello Sumaila

Ba za a taɓa haɗa gwamnatin Abba da ta baya ba wajen gudanar da ayyukan cigaba a Jihar Kano – Bello Sumaila

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Jigo a siyasar yankin Sumaila da ke Kudancin Jihar Kano, Hon. Bello Musa ɗan Jam'iyyar NNPP ya bayyana cewa yanayin ayyukan raya ƙasa da gwamnatin Abba Kabir Yusuf take masu kyau da inganci, ba za a kwatanta da gwamnatin APC ta Dakta Abdullahi Umar Ganduje ba. A lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano, Hon. Bello Musa ya ce, “Har ga Allah muna ganin bambanci sosai a wannan gwamnatin idan aka kwatanta ta da ta baya. Ayyuka ga su nan ana ta yi i babu dare, ba rana a ko’ina ga hanyoyi ta…
Read More
Uba Sani da Yerima Shettima ƙungiyar Capacity Movement ta ɗauka zuwa yanzu – Sani Sado

Uba Sani da Yerima Shettima ƙungiyar Capacity Movement ta ɗauka zuwa yanzu – Sani Sado

Daga ABBA MUHAMMAD a Kaduna  ƙungiyar Capacity Movement, ƙarƙashin jagorancin shugaban ta na ƙasa Alhaji Shehu Sani Sado, ta yi ƙarin haske kan jita-jita, tambayoyin jama’a da kafafen yaɗa labarai ke yi dangane da matsayar ta a siyasa yayin da harkokin siyasar Jihar Kaduna ke ƙara ɗumama. A matsayin ta na ƙungiyar da ta ginu a kan gaskiya, jama’a da tsari mai nagarta, hakan ya sa, ya zama wajibi ta jaddada matsayar ta a fili. Sanarwar mai ɗauke da sa hannun sakataren ƙungiyar a ƙasa, Dakta Bashir Umar Mohammed ta ce, “A halin yanzu, bayan Ambasada Yerima Usman Shettima da…
Read More
NNPP ta zargi Kwankwaso da yin sanadiyyar fitar Kofa da Oguntoyinbo daga jam’iyyar 

NNPP ta zargi Kwankwaso da yin sanadiyyar fitar Kofa da Oguntoyinbo daga jam’iyyar 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta ce ficewar dan majalisa Abdulmuni Jibrin Kofa zuwa jam’iyyar APC da kuma Amb. Oluremi Oguntoyinbo zuwa jam’iyyar PDP ta faru ne sakamakon zagon ƙasa da cin amana da Sanata Rabiu Kwankwaso ya aikata. Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a cikin martaninta kan sauyin sheka da wasu daga cikin mambobinta suka yi zuwa jam’iyyar APC mai mulki da kuma PDP. A tuna cewa, Kofa, a ranar Litinin, ya sanar da komawarsa jam’iyyar APC tare da bayyana goyon bayansa ga takarar Shugaba Bola Tinubu a 2027. Haka kuma, tsohon…
Read More
Ƙaramar Hukumar Mai’adua ta bada Naira Miliyan 30 ga masu ƙananan sana’o’i

Ƙaramar Hukumar Mai’adua ta bada Naira Miliyan 30 ga masu ƙananan sana’o’i

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Tallafin kuɗin za a raba shi ga matasa maza da mata masu ƙananan sana'o'i su 3000 da suka fito daga lungu da saƙo na karamar hukumar Mai'adua, inda ko wannan su zai amfana da kudi Naira 10,000. Da yake gabatar da jawabin shi gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa ta bakin Hon. Ibrahim Yusuf Jirdede ya bayyana cewa" Tallafin kuɗin zai taimaka ma masu ƙananan sana'o'i domin su yi dogaro da kai. Ya yabawa shugaban ƙaramar hukumar akan bada tallafin kuɗin ga al'ummar shi domin dogaro da kai. "Wannan abin alheri babu shakka zai taimaka…
Read More
Zaɓen ƙananan hukumomi: APC ta lashe dukkan ƙananan hukumomin Neja 

Zaɓen ƙananan hukumomi: APC ta lashe dukkan ƙananan hukumomin Neja 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Jam’iyyar APC mai mulki ta lashe dukkan kujerun shugabannin kananan hukumomi a zaben da aka gudanar a ƙananan hukumomi 25 na jihar Neja. Haka kuma jam’iyyar ta lashe kujerun kansiloli 271 daga cikin 274 da ake takara a fadin kananan hukumomin, yayin da jam’iyyar adawa ta PDP ta samu kujeru uku kacal – biyu a karamar hukumar Tafa da daya a Rafi. An gudanar da zaɓen ne a ranar 1 ga Nuwamba, inda fiye da jam’iyyu 10 suka tsaida ‘yan takara don neman mukamai daban-daban. Cikin jam’iyyun da suka shiga zaben akwai PDP, APGA,…
Read More