Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Jam’iyyar NNPP ta sake zaɓen Ajuji Ahmed a matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa.
An sake zaɓen Ahmed ne a ranar Asabar a babban taron jam’iyyar na ƙasa da aka gudanar a Abuja, inda zai yi wa’adin shekaru huɗu karo na biyu.
NNPP ta kuma sake zaɓen sauran mambobin kwamitin gudanarwa na kasa, ciki har da Abba Kawu, mataimakin shugaban jam’iyyar na arewa; Onu Nwaze, mataimakin shugaban jam’iyyar na kudu; Dipo Olayokun, sakataren ƙasa; da Oladipo Johnson, sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar.
Sauran sun haɗa da Ibrahim Muhammad, mataimakin sakataren ƙasa; Bala Mohammed, sakataren tsare-tsare na ƙasa; Ahmed Balewa, ma’aji na ƙasa; Akpan Ekan, sakataren kuɗi na ƙasa; Maryam Yasin, shugabar mata ta ƙasa; Muhammad Musa, shugaban matasa na ƙasa; Magaji Ibrahim, mai ba da shawara kan shari’a na ƙasa; da Mustapha Danhajia, sakataren walwala na ƙasa.
Haka kuma akwai Sadiƙ Abubakar, mai binciken kuɗi na ƙasa; Bashir Abacha, jami’in hulɗa na ƙasa; Shehu Bello, mataimakin shugaban jam’iyyar na shiyyar Arewa maso Yamma; Abubakar Abdulrahman, mataimakin shugaban jam’iyyar na Arewa ta Tsakiya; Stanley Ijeh, mataimakin shugaban jam’iyyar na Kudu maso Kudu; Ademola Ayaode, mataimakin shugaban jam’iyyar na Kudu maso Yamma; Collins Onuoha, mataimakin shugaban jam’iyyar na Kudu maso Gabas; da Abdulrahman Auwal, wakilin masu bukata ta mussaman.
An kuma zaɓi Moses Okoh, mataimakin sakataren tsare-tsare na ƙasa; Solape Olatuboson, mataimakiyar shugabar mata ta ƙasa; Fredrick Mbasi, mataimakin shugaban matasa na ƙasa na 1; Chidiobi Jenny, mataimakin shugaban matasa na ƙasa na 2; Fatai Batola, mataimakin sakataren walwala na ƙasa; Bush Adomson, mataimakin mai binciken kuɗi na ƙasa; Saleh Bade, mataimakin sakataren kuɗi na ƙasa; da Chubisi Emmanuel, mataimakin ma’aji na ƙasa.
Shugaban kwamitin shirya babban taron jam’iyyar na ƙasa, Bala Mohammedo, ya ce an gudanar da zaɓen ne bisa ƙa’ida da kuma dokoki da ƙa’idodin Hukumar Zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC).
A nasa jawabin, Ahmed ya ce an “sake tsugunar da jam’iyyar, an sake tsarata kuma an ƙarfafa ta” a matsayin babbar mai ruwa da tsaki a tsarin dimokiraɗiyyar ƙasar nan.
Ya ce, “Idanun kowa na kan babbar jam’iyyarmu domin nuna hanyar da za a bi wajen samun dimukraɗiyya mai ɗorewa da ci gaba a Nijeriya .”
Shi ma da yake jawabi, Rabiu Kwankwaso, tsohon gwamnan Kano kuma jagoran NNPP, ya yaba wa zaɓaɓɓun jami’an tare da yi musu kira da su kasance masu ladabi da biyayya ga jam’iyyar.
