Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana cewa ba zai goyi bayan sake tsayawar Shugaba Bola Tinubu takara a 2027 ba, yana mai gargaɗin cewa raunana jam’iyyar PDP na iya barazana ga dimokuraɗiyyar Nijeriya.
Makinde ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai a Ibadan, inda ya ce a wani taro da ya halarta tare da Shugaba Tinubu da Ministan Abuja, Nyesom Wike, Wike ya yi tayin “riƙe PDP” domin Tinubu gabanin zaɓen 2027, ba tare da an nemi hakan ba.
Ya ce duk da cewa Wike na da ’yancin mara wa Tinubu baya, shi kansa ya zaɓi kada ya yi haka, yana mai kira ga ’yan Nijeriya da su kare tsarin dimokuraɗiyyar jam’iyyu da dama, su kuma ƙi duk wani shiri na jam’iyya ɗaya.
Makinde ya kuma bayyana cewa yana da gogewa da cancantar tsayawa takarar Shugaban ƙasa a 2027, yana mai ambaton wa’adinsa biyu a matsayin gwamnan Oyo da gogewarsa a harkar kasuwanci.
Haka kuma ya ce abin da ya fi mayar da hankali a kai shi ne gina ƙaƙƙarfan tsare-tsare da cibiyoyi fiye da gina manyan ayyukan more rayuwa kawai.
