Uba Sani da Yerima Shettima ƙungiyar Capacity Movement ta ɗauka zuwa yanzu – Sani Sado

Spread the love

Daga ABBA MUHAMMAD a Kaduna 

ƙungiyar Capacity Movement, ƙarƙashin jagorancin shugaban ta na ƙasa Alhaji Shehu Sani Sado, ta yi ƙarin haske kan jita-jita, tambayoyin jama’a da kafafen yaɗa labarai ke yi dangane da matsayar ta a siyasa yayin da harkokin siyasar Jihar Kaduna ke ƙara ɗumama. A matsayin ta na ƙungiyar da ta ginu a kan gaskiya, jama’a da tsari mai nagarta, hakan ya sa, ya zama wajibi ta jaddada matsayar ta a fili.

Sanarwar mai ɗauke da sa hannun sakataren ƙungiyar a ƙasa, Dakta Bashir Umar Mohammed ta ce, “A halin yanzu, bayan Ambasada Yerima Usman Shettima da mai girma gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, Capacity Movement ba ta yi wani ƙarin goyon baya ga kowanne ɗan siyasa ba.”

Shehu Sani Sado, ya ce, “Duk wani matakin siyasa da ƙungiyar za ta ɗauka dole ne ya yi daidai da ƙa’idoji na ƙungiyar.”

Ya kuma jaddada cewa goyon baya ba abin wasa ba ne, ba kuma abin da ake yin sa saboda matsin lamba, maslahar siyasa, ko son rai ba. Ana yin shi ne kawai bisa hujjar ingantaccen aiki, kyakkyawar halayya, da tsantsar jajircewa ga ci gaban al’umma.

A cewarsa, Ambasada Yerima Usman Shettima na wakiltar irin nagartaccen jagoranci da ƙungiyar ke goyon baya. Shekarun sa a gwagwarmaya, haɗa kan matasa, shiga al’amuran ƙasa da kyakkyawar mu’amala da al’umma sun ba shi martaba a faɗin Nijeriya da cikin ƙungiya. Aƙidar sa na jagoranci na da cikakkiyar alaƙa da manufofin ƙungiyar Capacity Movement, musamman a fannin adalci, kare haƙƙin bil’adama da ci gaban al’umma.

Haka kuma, Gwamna Uba Sani ya nuna bajin ta a mulkin jinƙai da ke da nasaba da jama’a. Gudunmawarsa ta ɓangaren walwalar jama’a, tallafi ga marasa ƙarfin tattalin arziki, tsaro, ƙarfafa al’umma da ci-gaban tattalin arziki sun bayyana irin jagorancin da Capacity Movement ke maraba da shi. Hankalin sa da saurin amsa buƙatun jama’a da manufofin sa na haɗin kai sun ƙara tabbatar da shi a matsayin jagora nagartacce kuma mai sauƙin kai a Jihar Kaduna.

Duk da waɗannan manyan mutane biyu da aka tabbatar, ƙungiya ta sake nanatawa cewa babu wani ɗan siyasa daban da aka amince da shi a kowane mataki a halin yanzu bayan su biyun. 

Don haka duk wata magana ko jita-jitar da ake yaɗawa game da wani goyon baya daban, ba gaskiya ba ne kuma ba daga ƙungiyar ta fito ba.

Alhaji Sado ya ƙara da cewa ƙungiya za ta ci-gaba da bibiyar yanayin siyasar ƙasa a hankali. Duk wani goyon baya a nan gaba za a yi shi ne bayan cikakken nazari da shawara mai zurfi domin tabbatar da cewa ya dace da buƙatun jama’a da ƙimar ƙungiyar Capacity Movement.

ƙungiyar ta yi kira ga magoya baya, masu ruwa da tsaki, kafafen yaɗa labarai da jama’a baki ɗaya da su rinƙa dogaro da bayanai daga shugabanin ƙungiyar kaɗai idan ana neman gaskiya kan goyon baya, haɗin kai ko alaƙar siyasa. Burin mu shi ne gaskiya, jama’a, da ingantaccen jagoranci a faɗin Nijeriya.

ƙungiyar Capacity Movement wata ƙungiya ce da ka assasa ta don zaƙulo nagartattun ‘yan siyasa a Nijeriya da za su jagoranci ƙasar a kowane mataki. A halin yanzu ƙungiyar ta fara karaɗe kowa ina, kuma ta na ƙara samun karɓuwa a wajen jama’a.

By ukarofi