Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Tallafin kuɗin za a raba shi ga matasa maza da mata masu ƙananan sana’o’i su 3000 da suka fito daga lungu da saƙo na karamar hukumar Mai’adua, inda ko wannan su zai amfana da kudi Naira 10,000.
Da yake gabatar da jawabin shi gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa ta bakin Hon. Ibrahim Yusuf Jirdede ya bayyana cewa” Tallafin kuɗin zai taimaka ma masu ƙananan sana’o’i domin su yi dogaro da kai.
Ya yabawa shugaban ƙaramar hukumar akan bada tallafin kuɗin ga al’ummar shi domin dogaro da kai.
“Wannan abin alheri babu shakka zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arziki da rage talauci ga al’ummar ƙaramar hukumar,”inji wakilin gwamnan.
Jawabin sa shugaban ƙaramar hukumar Hon. Mamman Salisu Na Allahu ya bayyana cewa” Tallafin da aka bayar somin taɓi ne, a cewar sa nan bada jimawa ba, akwai ƙarin tallafi da al’ummar yankin za su amfana.
Ya bayyana cewa ya zuwa yanzu ƙaramar hukumar ta aiwatar da ayyuka da dama na raya ƙasa, wanda suka haɗa da gyaran Asibitoci, Makarantu, magudanan ruwa, gyaran makabartu da dai sauran su.
Shugaban ƙaramar hukumar ya yi kira ga wanda suka amfana da tallafin da su yi amfani dashi yadda ya dace, kadda su kalli ƙanƙantar kuɗin, ya tabbatar da cewa zai cigaba da bada wannan tallafi ga irin waɗannan matasa da mata masu sana’o’i a yankin.
Haka kuma ya yi kira ga al’ummar ƙaramar hukumar da su ba gwamnatin malam Dikko Raɗɗa da shi kan sa goyon baya da yi masu addu’ar sauke nauyin da aka ɗora masu.
Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da shugaban ƙungiyar ma’aikata ƙananan hukumomin ta jihar Kwamared Nasir Wada Mai’adua da mai ba gwamna shawara akan harkokin siyasa Rt. Hon Yau Umar Gwajo Gwajo da dai sauran su.
