Siyasa

Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta keɓe yanke hukunci kan shari’ar zaɓen gwamnan Nasarawa

Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta keɓe yanke hukunci kan shari’ar zaɓen gwamnan Nasarawa

Kotun Ƙoli ta keɓe yanke hukunci kan shari'ar zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa da ke gabanta. Kotu ta yi hakan ne a zaman ci gaba da sharilar da ta yi a wannan talatar. Ta ce za ta sanar da bangarorin da shari'ar ta shafa ranar da za raba gardama idan ta tsayar da rana nan gaba. Ana fafata shari'ar ne tsakanin Gwannan jihar, Injiniya Abdullahi Sule da kuma Jam'iyyar PDP a jihar tare da dan takararta na gwamna, David Ombugadu
Read More
Buni ya samar da romon dimukraɗiyya a Nengere – Hon. Yerima

Buni ya samar da romon dimukraɗiyya a Nengere – Hon. Yerima

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Karamar Hukumar Nengere a Jihar Yobe, Hon. Salisu Yerima ya bayyana irin kokarin da Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya yi wajen samar da romon dimukradiyya ga al'ummar yankin tun bayan hawansa mulkin jihar a 2019. Hon. Yerima ya ce Gwamna Buni ya yi abin a yaba da irin jagorancinsa na cire kyashi wajen dorawa daga inda tsohon gwamnan jihar, kuma Ministan Harkokin 'Yan Sanda na yanzu, Sanata Ibrahim Geidam ya tsaya. Ya ce an samu nasarori masu tarin yawa da suka haifar wa jihar da mai ido, inda ya ce shirye-shiryen…
Read More
Kotun Ƙoli ta yi fatali da ƙarar PDP kan nasarar Gwamnan Benuwe 

Kotun Ƙoli ta yi fatali da ƙarar PDP kan nasarar Gwamnan Benuwe 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kotun Koli ta yi fatali da karar da aka daukaka kan zaben gwamna Hycinth Alia na jihar Benuwai. Matakin na zuwa ne bayan janye karar da lauyan Mr Titus Uba na Jam'iyyar PDP, Sebastian Hon ya yi. Titus Uba ya kalubalanci nasarar gwamna Hyacinth ne na jam'iyyar APC. Sai dai kotun kararrakin zabe da ta daukaka kara a Abuja sun tabbatar Alia ne halastaccen gwamnan jihar ta Benue bayan da hukumar zabe INEC ta ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaben ranar 18 ga watan Maris. Kotun daukaka karar ta ce…
Read More
Gwamnonin G5 na PDP za su mara wa Tinubu baya a 2027 – Ortom

Gwamnonin G5 na PDP za su mara wa Tinubu baya a 2027 – Ortom

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Gwamnan Jihar Benuwe, Samuel Ortom ya ce, gwamnonin G5 na Jam’iyyar PDP za su sake marawa takarar Shugaban Kasa Bola Tinubu baya a 2027 idan ya ce zai sake tsaya wa takara. Mista Ortom ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi yayin wata liyafar cin abinci ta murnar shiga sabuwar shekara da ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya shirya a Jihar Ribas. Gwamnonin G5 sun hada da Mista Ortom, Mista Wike, tsohon gwamnan Jihar Inugu, Ifeanyi Ugwuanyi, tsohon gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu, da gwamnan Jihar Oyo Seyi Makinde. Mista Ortom…
Read More
Mun yi na’am da hukunce-hukuncen Kotun Ƙoli – APC

Mun yi na’am da hukunce-hukuncen Kotun Ƙoli – APC

Daga BASHIR ISAH Jam’iyyar APC ta ce ta yi na’am da hukunce-hunkuncen da Kotun Koli ta yanke kan kararrakin da aka daukaka na kalubalantar sakamakon zaben gwamnoni na 2023 a jihohi guda takwas. APC ta bayyana gamsuwarta ne cikin sanarwar da ta faitar ranar Juma’a mai dauke da sa hannun Sakataren Yada Labarai na Kasa, Felix Morka. Jam’iyyar ta ce ta yi matukar farin ciki kan yadda kotun ta tabbatar da nasarar da ‘ya’yanta kuma gwamnonin Legas, Ebonyi Kuros Riba suka samu a zaben 2023 da ya gabata. Morka ya ce duk da dai APC ta fadi a shari’ar  Kano,…
Read More
Na yi ritaya daga siyasa, cewar Abdullahi Adamu

Na yi ritaya daga siyasa, cewar Abdullahi Adamu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce ya yanke shawarar barin harkokin siyasa, inda ya ce ya lura cewa siyasa ta fita daga ran sa. Adamu ya bayyana haka ne a wajen ƙaddamar da wani littafi mai suna ‘Progressive Governance, Showcasing The Achievements of Governor Abdullahi Sule of Nasarawa State 2019–2023’ wanda Abdullahi Tanimu ya wallafa. Tsohon shugaban jam’iyyar APC ɗin, wanda shi ne gwamnan farar hula na farko a jihar, kuma ya yi mulki a tsakanin 1999 zuwa 2007, yayin da yake magana kan littafin mai shafuka 230, ya…
Read More
Kotun Ƙoli ta ɗage yanke hukunci kan zaɓen Gwamnan Kano

Kotun Ƙoli ta ɗage yanke hukunci kan zaɓen Gwamnan Kano

Daga BASHIR ISAH Kotun Ƙoli ta ɗage yanke hukuncin zaɓen gwamnan Kano zuwa wani lokaci da ba ta ambata ba. Zaman da Kotun ta yi mai alƙalai biyar a ranar Alhamis, ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a Inyang Okoro. A ranar 17 ga Nuwamban 2023 Gwamnan Kano, Abba Yusuf da Jam'iyyarsa ta NNPP suka ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli inda suke ƙalubalantar hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara da ta soke nasarar da Gwamna Abba ya samu a zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ran 19 ga Maris. Kazalika, jam'iyyar ta nusar da Kotun Ƙolin dambarwar da ta auku a hukuncin…
Read More
Lalong ya sha rantsawar zama Sanatan Filato ta Kudu

Lalong ya sha rantsawar zama Sanatan Filato ta Kudu

Daga BASHIR ISAH An rantsar da tsohon Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong, a matsayin sanata mai wakiltar Filato ta Kudu a Majalisar Dattawan Nijeriya. Lalong ya yi murabus ne daga muƙamin Ministan Ƙwadago a gwamnatin Tinubu sannan ya maye gurbin Napoleon Bali na Jam'iyyar PDP wanda Kotun Ɗaukaka Ƙara ta sauke shi biyo bayan ƙarar da Lalong ya shigar a kansa a kotun sauraren ƙararrakin zaɓe. Akawun majalisar, Chinedu Akubueze, shi ne ya rantsar da Long yayin zaman majalisar a ranar Laraba ƙarƙashin jagorancin Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio. Da yake jawabi jim kadan bayan rantsar da Lanlon a matsayin…
Read More
Fabrairu INEC za ta sake zaɓen wasu mazaɓu da na cike-gurbi – Shugaban INEC

Fabrairu INEC za ta sake zaɓen wasu mazaɓu da na cike-gurbi – Shugaban INEC

Daga BASHIR ISAH Ya zuwa watan Fabrairu na baɗi Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ke sa ran sake zaɓuɓɓuka a wuraren da akwai buƙatar haka a sassan ƙasa. Shugaban hukumar na ƙasa, Mahmoud Yakubu, shi ne ya bayyana haka a wajen taron da suka yi da jam'iyyum siyasa a ranar Litinin. “Game da zaɓen cike gurbi, idan ba a manta ba a jawabin da na yi a lokacin rantsar da Kwamishinonin Zaɓe (RECs) haɗe da taron zangon ƙarshe da muka yi da baƙi ɗaya kwamishinonin zaɓe na ƙasa, na ce hukumar za ta gudanar da zaɓe domin cike guraben da…
Read More
’Yan bindiga sun wawashe takardun kotun zaɓen gwamnan Kogi

’Yan bindiga sun wawashe takardun kotun zaɓen gwamnan Kogi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wasu 'yan bindiga sun kai hari kan magatakardan Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓen gwamnan Jihar Kogi, David Umar Mike, tare da kwashe takardun masu ƙara. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar (PPRO), SP William Aya, ya bayyana hakan a Lokoja ranar Laraba. Hukumomin 'yan sandan sun ce maharan da suka kai harin na sakatariyar kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar sun kwashe dukkanin takardun ƙarar da wasu jam’iyyun siyasa biyar suka shigar. A cewar hukumomin ’yan sanda, takardun da aka kwace daga hannun Mike sun haɗa da, ƙorafe-ƙorafen da jam’iyyu huɗu (4): Action Alliance…
Read More