Siyasa

INEC za ta samar da sabbin mazaɓu a faɗin Nijeriya kafin zaɓen 2023 – Mahmood Yakubu

INEC za ta samar da sabbin mazaɓu a faɗin Nijeriya kafin zaɓen 2023 – Mahmood Yakubu

Daga WAKILIN MU Nan da lokacin da za a gudanar da babban zaɓe a Nijeriya, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) za ta samar da ƙarin mazaɓu a faɗin ƙasar. Shugaban kwamitin wayar da kan masu zaɓe a hukumar (IVEC), Mista Festus Okoye, shi ne ya bayyana haka a Abuja. Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, a cikin Agustan 2014 INEC ta gabatar da buƙatar samar da ƙarin mazaɓu 30,027, inda arewacin ƙasar za ta samu mazaɓu 21,615 yayin da kudu za ta samu 8,412. Wannan ya janyo ce-ce-ku-cen da ya sa INEC ta watsar da shirin. Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ya…
Read More
Mun shirya wa yin zaɓen cike gurbi a Neja, cewar INEC da ‘yan sanda

Mun shirya wa yin zaɓen cike gurbi a Neja, cewar INEC da ‘yan sanda

Daga WAKILIN MU Kwamishinan Zaɓe mai zama a Jihar Neja (REC), Farfesa Samuel Egwu, ya ce Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta gama shiryawa tsaf domin gudanar da zaɓen cike gurbi da za a yi a Mazaɓar Tarayya ta Magama/Rijau da ke jihar a ranar Asabar, 6 ga Fabrairu, 2021. Egwu ya faɗi haka ne a ranar Alhamis lokacin da ya ke tattaunawa da wakilin Hukumar Dillancin Labarai ta Nijeriya (NAN) a Minna. Ya ce hukumar sa ta gama duk wani shirin yin zaɓe mai inganci da tsare gaskiya, domin kuwa ta horas da ma'aikatan zaɓe mutum 1,258 saboda zaɓen.  Ya…
Read More
An samu ɗimbin cigaba a ƙarƙashin APC – cewar Bello

An samu ɗimbin cigaba a ƙarƙashin APC – cewar Bello

Daga BASHIR ISAH Ministan Abuja Malam Muhammad Musa Bello ya ce, gwamnatin jam'iyyar APC ta samar da cigaba masu yawa tun bayan kama mulki a 2015. Bello ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin kwamitin shirin sabunta rijistar mambobin APC na Abuja a Alhamis da ta gabata. Yana mai cewa, "Waɗanda suke mazauna Abuja, ko masu yawan ziyartar ta a 2015, sun san akwai bambanci da Abuja ta wancan lokaci da ta yanzu." Daga nan, Bello ya nuna gamsuwarsa dangane da naɗa Hon. Sanda Umar Garba da aka yi a matsayin Shugaban Kwamitin Kula da Shirin Sabunta…
Read More
Buhari ya sabunta rijistarsa ta zama a APC

Buhari ya sabunta rijistarsa ta zama a APC

Daga FATUHU MUSTAPHA A ranar Asabar da ta gabata Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sabunta rijistarsa ta zama cikakken dan jam'iyyarsu ta APC, a mahaifarsa Daura da ke jihar Katsina. Tare da kira ga daukacin shugabannin jam'iyyar da karfafa kwazo wajen tabbatar da APC ta samu karin tagomashi a matakin farko. Buhari ya yi wannan kira ne a lokacin da ya karbi bakuncin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan da wasu gwamnoni hada da wasu 'ya'yan jam'iyyar APC a garin Daura, jim kadan bayan ya kammala sabunta rijistarsa ta jam'iyya a Gundumar Sarkin Yara. A wata sanarwa da mai magana…
Read More
Buhari ya tafi Daura don sabunta rijistar zama dan APC

Buhari ya tafi Daura don sabunta rijistar zama dan APC

Daga FATUHU MUSTAPHA Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi tafiya zuwa mahaifarsa Daura, da ke jihar Katsina. Buhari ya yi wannan tafiya ne a Juma'ar da ta gabata domin sabunta rajistar zama mamba a jam'iyyar APC wanda jam'iyyar ke shirin somawa a fadin kasa. Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masara da Mataimakin Kakin Majalisar Dokokin jihar da sauransu, na daga cikin wadanda suka tarbi shugaban bayan da ya isa Babban Filin Jirgin Sama na Umaru Musa Yar’Adua da ke Katsina. A bangare guda, Sarkin Daura Alhaji Faruk Umar Faruk, ya jagoranci dakatai da sauran su, inda suka ziyarci Buhari a…
Read More