Buhari ya sabunta rijistarsa ta zama a APC

Daga FATUHU MUSTAPHA

A ranar Asabar da ta gabata Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sabunta rijistarsa ta zama cikakken dan jam’iyyarsu ta APC, a mahaifarsa Daura da ke jihar Katsina. Tare da kira ga daukacin shugabannin jam’iyyar da karfafa kwazo wajen tabbatar da APC ta samu karin tagomashi a matakin farko.

Buhari ya yi wannan kira ne a lokacin da ya karbi bakuncin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan da wasu gwamnoni hada da wasu ‘ya’yan jam’iyyar APC a garin Daura, jim kadan bayan ya kammala sabunta rijistarsa ta jam’iyya a Gundumar Sarkin Yara.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugban, Garba Shehu ya fitar, Buhari ya ce za a iya cim ma wannan kudiri muddun shugabannin jam’iyyarsu suka gyara damara game da sha’anin yin rijistar da sabunta ta a matakin unguwanni da kananan hukumomi da jihohi da ma matakin kasa hada da birnin Tarayya, Abuja.

A cewar Buhari, “Ina mika godiyata gare ku dangane da halartowar da kuka yi don kaddamar da shirin yin rijista na jam’iyyarmu. Zuwanku na da matukar muhimmanci saboda hakan zai kara wa jam’iyyar armashi da kuma taimaka mata wajen samun sabbin mambobi.

“Ina godiya da irin wannan tsarin yin rijista da kuka zaba, wanda zai soma daga matakin unguwanni zuwa matakin kasa, har da Abuja.

“Salo da tsarin rijista a jam’iyyarmu kada ya ci gaba da kasancewa daga sama za a soma zuwa kasa, sai dai daga kasa zuwa sama domin bai wa jama’a cikakkiyar damar kare jam’iyyarsu a kowane mataki.

“Zamanin jawo ra’ayin mutane da kudi don shiga jam’iyya ya wuce, saboda ba mu da kudi.”

Daga nan, Buhari ya yi kira ga masana a fadin kasa da su rinka kwatanta adalci wajen auna ayyukan gwamnati, kuma a zama masu yabawa da kokarin gwamnati. Saboda a cewarsa, ko da suka shigo sun tarar da tattalin arzikin kasa cikin wani hali mara kyau wanda sai da ya kai ga an tallafa wa jijohi da rance kafin suka iya tabuka wani abu.

Daga nan, ya yi kira ga daukacin magoya bayan APC da a je a sabunta rijista, haka ma masu sha’awar shiga jam’iyyar su je su yi rijista, kana a kiyaye dokokin kariya daga cutar korona yayin da ake kokarin yin rijistar.

Da yake jawabi, Shugaban Kwamitin Riko na Kasa na APC kuma Gwamnan Yobe Mai Mala Buni, ya ce, sun riga sun kafa kwamiti guda biyu don tabbatar da sha’anin yin rijistar ya gudana yadda ya kamata.

Yana mai cewa, “Kwamitin farko shi ke da alhakin kula da wayar da kan al’umma karkashin jagorancin Gwamna Yahaya Bello. Sannan daya kwamitin an dora masa aikin kula da sha’anin yin rijistar, karkashin jagorancin Gwamnan Neja Abubakar Bello.”

Buni ya fada shaida wa Buhari cewa, “Muna alfahari da kai. Kai mutum na musamman da Allah Ya yi amfani da shi wajen daidaita lamarin Nijeriya a lokacin da ta fada tsaka-mai-wuya.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *