Rattaba wa dokar NOUN hannu da na yi ya haifar wa dalibanta samun tagomashi – Buhari

Daga AISHA ASAS

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, rattaba hannu da ya yi a dokar Budaddiyar Jami’ar Nijeriya (NOUN) da aka yi wa gyaran fuska, ya haifar wa jami’ar da ɗalibanta samun tagomashi a kasa.

Shugaban ya bayyana haka ne yayin bikin yaye daliban jami’ar karo na 9 da na 10 da aka hade wuri guda wanda ya gudana ta bidiyo a ranar Asabar da ta gabata.

Da yake jawabi yayin bikin ta bakin wakilinsa Mataimakin Sakataren Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa, Ramon Yusuf, Buhari ya ce, “Budaddiyar Jami’ar tana sauke nauyin da ya rataya a kanta na saukaka wa ‘yan Nijeriya sha’inin neman ilimi.”

Sanarwar da ta fito ta hannun Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Jami’ar, Malam Ibrahim Sheme, ta nakalto Buhari na cewa, gwamnatinsa ta bai wa fannin ilimi muhimmanci musamman ta fuskar tabbatar da ‘yan kasa na iya yin karatu ko daga gida.

Daga nan, Buhari ya yaba wa kokarin hukumar jami’ar a ci gaba da samar wa ‘yan kasa damarmakin karatu da take yi. Tare da bayyana jami’ar a matsayin jami’a daya tilo a Nijeriya mai ba da zarafin yin karatu daga gida.

A nasa bangare, Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Abdalla Uba Adamu, ya ce bikin yayewar ya shafi dalibai 32,725 ne da suka nazarci kwasa-kwasai daban-daban a jami’ar.

Adamu, wanda ke shirin kammala wa’adin shekaru biyar na jagorancin jami’ar a Fabrairun 2021, ya bayyana cewa, dalibai 24,300 ya kamata a yi wa bikin yayewa a 2020 amma sai hakan bai yiwu ba saboda dokar kulle da aka kafa a dalilin cutar korona.

Ya ce, idan aka hada da daliban da suka kammala karatu a 2021 su 8,425, wannan shi ya ba da adadin dalibai da aka yaye su 80,418 a tsakanin shekaru biyar da jami’ar ta yi a karkashin kulawarsa.

Da yake tofa albarkacin bakinsa a wajen bikin, Shugaban Jami’ar Mai Martaba, Ambasada (Dr.) Lawrence O.C. Agubuzu, ya yaba wa Gwamnatin Tarayya bisa irin gudunmawar da ta bai wa jami’ar.

Haka shi ma Shugaban Hukumar Gudanarwar Jami’ar, Farfesa Peter Okebukola, ya bayyana bikin a matsayin abin da zai zama abin koyin ga sauran jami’o’i a fadin kasar nan.

Dubban ‘yan’uwa da abokai na daliban da lamarin ya sha ne suka shaida bikin ta bidiyo. Haka ma jami’ar ta samu sakonnin fatan alheri da dama daga takwarorinta a sassa daban-daban.