Cutar Korona: Za a tabbatar da kiyaye dokokin kariya a Abuja – Minista

Daga WAKILINMU

Hukumar Birnin Tarayya, Abuja ta ce, za ta tabbatar da an bi dokokin yaki da Cutar Korona na 2021 kamar yadda Kwamitin Shugaban Kasa Kan Yaki da Cutar Korona ya shimfida.

Hukumar ta bayyana haka ne a wajen wani taron masu fada a ji da ya gudana a karkashin jagorancin Ministan Abuja, Malam Muhammad Musa Bello, a Juma’ar da ta gabata a Abuja.

Da yake jawabi yayin taron, Ministan Abuja ya ce, “Za a kara himma wajen wayar da kan mazauna Abuja game da kiyaye dokokin yaki da Cutar Korona, tare da tabbatar da an hukunta duk wanda aka samu da take dokokin ta hanyar amfani da kotunan tafi-da-gidanka.”

A cewar hukumar, ta fahimci cewa motocin kasuwa na daga cikin manyan hanyoyin yada cutar korona, don haka ta ce za ta hada kai da ‘yan yuniyan domin cim ma kudirinta.

Duka wadannan bayanai na kunshe ne cikin wata sanarwa da ta fito ta hannun Babban Sakataren Yada Labarai na Hukumar Abuja, Mr Anthony Ogunleye, mai dauke da kwanan wata 29 ga Janairun 2021.

Mahalarta taron sun hada da Ministan Abuja, Malam Muhammad Musa Bello, da Karamar Ministar Abuja, Dr Ramatu Tijjani Aliyu, da Babban Sakataren Hukumar Abuja, Mr Olusade Adesola, ‘yan siyasa, sarakunan gargajiya da dai sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *