Bauchi: Daliban makarantun kudi na iya neman gurbin karatu a makarantun gwamnati – Tilde

Daga FATUHU MUSTAPHA

Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Bauchi ta bayyana cewa, dalibai daga makarantun sakandare masu zaman kansu a jihar na iya neman gurbin karatu a makarantun gwamnatin jihar don shiga aji hudu (SS1).

Kwamishinan Ilimi na Jihar, Dr. Aliyu I. Tilde ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a wannan Asabar.

A cewar kwamishinan, “Mun fahimci cewa iyaye kalilan ne da ‘ya’yansu ke tafiya makarantun kudi ke da masaniyar cewa ‘ya’yansu na da damar neman gurbin karatu a makarantun sakandaren gwamnatin jihar don shiga aji hudu ta hanyar amfani da sakamakonsu na BECE.”

Ya ci gaba da cewa, “Za a nemi damar haka ne ta hanyar rubuta wa Kwamishinan Ilimi na Jihar Bauchi takarda.

“Za a karbi dalibi ne ta hanyar la’akari da sakamakonsa na BECE, inda dalibi ya fito da sauransu.”

Tilde ya bukaci iyayen yara su sanya inda suke da zama a takardar da za su rubuta saboda hakan zai taimaka musu wajen sanya yaro a makarantar da ta fi kusa da gida ko unguwarsu. Yana mai cewa, tuni wasu makarantu irin su Saadu Zungur da Bakari Dukku da Ibrahim Bako sun cika, babu sauran gurbin da za a iya karbar dalibai.

“Haka nan, za a iya neman gurbin karatu a wadannan makarantu: GGDSS Alkaleri, GGDSS Zaki, GDSS Bogoro, GDSS Dagauda, GDSS Darazo, GDSS Madara, GDSS Burra, GDSS Giade, GDSS Duguri, GDSS Itas, GDSS Chinade, GDSS Gamawa da kuma GDSS Udubo”, inji Tilde.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *