Cutar Korona: Mutum 27 sun mutu a tsakanin sa’o’i 24 a Nijeriya

Daga UMAR M. GOMBE

Cibiyar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) ta bayyana cewa, an samu rasuwar mutum 27 cikin sa’o’i 24 a fadin kasa sakamakon Cutar Korona.

Cibiyar ta sanar da hakan ne a shafinta na intanet a Juma’ar da ta gabata, inda ta ce kawo yanzu adadin wadanda suka mutu a fadin kasa a dalilin korona ya cilla zuwa mutum 1,557.

Kazalika, NCDC ta sanar an samu karin mutum 1,114 da suka harbu da cutar ta korona a fadin kasa.

Wanda a cewarta, “Ya zuwa yanzu mutum 128,674 ne aka tabbatar sun kamu da cutar a fadin kasa.”

Karin da NCDC ta ce an samu, ya shafi wasu jihohin kasar nan su 21 ne hada da birnin tarayya, Abuja.

Jihohin da karin ya shafa sun hada da: Lagos 408, FCT 95, Plateau 90, Ondo 66 da kuma Kaduna mai mutum 63.

Sauran su ne; Oyo 56, Borno 46, Imo 42 Edo 41, Ogun 37, Kano da Akwa Ibom kowacce 18, haka ma Delta da Osun kowacce 15, sai kuma Rivers mai mutum 31 da dai sauransu.

Bugu da kari, cibiyar ta ce mutum 1,269 ne aka sallama a fadin kasa bayan an yi musu magani sun warke a tsakanin sa’o’i 24 da suka gabata.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa ya ruwaito cewa, tun bullar korona a kasa a Fabrairun 2020 zuwa yau, an samu gwada samfur na mutum 1,270,523.

Sannan akwai mutum 24,317 masu dauke da cutar a fadin kasa da ake ci gaba da ba su kulawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *