NUJ ta yi rashi a Binuwai

Daga AISHA ASAS

Allah Ya yi wa Shugabar Kungiyar ‘Yan Jarida ta Jihar Benue, Comrade Victoria Asher, rasuwa.

Asher ta rasu ne bayan da aka yi mata aiki ta haifi tagwaye.

A sanarwar da sakataren NUJ na jihar, Moses Akarhan, ya fitar a wannan Asabar din, ta nuna Asher ta rasu ne da misalin karfe 8 na safiyar Asabar a asibitin FMC da ke Makurdi bayan da aka yi mata aiki.

Tuni dai gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya bayyana kaduwarsa game da rasuwar.

Kana ya yi fatan Allah ya bai wa iyalan marigayiyar juriya da danganar rashin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *