Buhari ya tafi Daura don sabunta rijistar zama dan APC

Daga FATUHU MUSTAPHA

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi tafiya zuwa mahaifarsa Daura, da ke jihar Katsina.

Buhari ya yi wannan tafiya ne a Juma’ar da ta gabata domin sabunta rajistar zama mamba a jam’iyyar APC wanda jam’iyyar ke shirin somawa a fadin kasa.

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masara da Mataimakin Kakin Majalisar Dokokin jihar da sauransu, na daga cikin wadanda suka tarbi shugaban bayan da ya isa Babban Filin Jirgin Sama na Umaru Musa Yar’Adua da ke Katsina.

A bangare guda, Sarkin Daura Alhaji Faruk Umar Faruk, ya jagoranci dakatai da sauran su, inda suka ziyarci Buhari a gidansa don yi masa maraba da zuwa.

Idan dai za a iya tunawa, kasa da wata biyu kenan da Buhari ya ziyarci Daura, a ranar 11 ga Disambam 2020.