‘Yan sanda sun cafke ƙasurgumin ɗan bindiga, Ali Bahago a Zamfara

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ta sanar da cafke wani fitaccen jagoran ‘yan bindiga mai suna Ali Bahago Danakulu tare da wasu mutum uku da ake zargi daga dabar sa. Kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya ce an gudanar da samamen ne bayan samun sahihan bayanan sirri kan ayyukan wasu masu aikata laifuka da ke addabar al’ummomin Kasuwan Daji da kewaye.

A cewar rundunar, waɗanda aka kama sun haɗa da Ali Bahago Danakulu, Hassan Dan Kure da Dahiru Lawali. Binciken farko ya nuna cewa suna cikin wata ƙungiyar masu garkuwa da mutane da aikata fashi da makami da sauran munanan laifuka a yankin Ƙaura Namoda da sauran sassan jihar.

‘Yan sanda sun bayyana cewa an kashe wani da ake zargi ɗan ne ƙungiyar yayin gudanar da samamen, yayin da aka samu nasarar cafke sauran waɗanda ake zargin. Haka kuma, an ƙwato makamai da kayayyaki daban-daban da suka haɗa da bindigar pump-action, bindiga kirar G3 da aka ƙera a gida, bindigogin Dane guda biyu, harsasai, da kuma babura uku ƙirar Boxer.

Rundunar ‘yan sandan Zamfara ta ce ana ci gaba da bincike domin gano cikakken girman ayyukan ƙungiyar da kuma cafke sauran yan bindigar da suka tsere. Ta kuma buƙaci al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro haɗin kai ta hanyar samar da sahihan bayanai domin ƙarfafa yaƙi da ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka a faɗin jihar.

By ukarofi

Leave a Reply