Daga ABUBAKAR A BOLARI GOMBE
Ma’aikatan kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano (KEDCO) sun tara sama da naira miliyan 23 domin tallafa wa kamfen ɗin takarar gwamna na Dokta Jamilu Isyaku Gwamna, ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a Jihar Gombe.
An bayyana hakan ne a wani taron karramawa da ma’aikatan kamfanin suka shirya masa, inda suka ce gudummawar ta samo asali ne daga godiyar da suke yi masa bisa damar aikin yi da ya samar wa mutane da dama lokacin da yake jagorantar kamfanin a matsayin Manajan Darakta.
Shugaban kwamitin shirya taron, Sa’idu Sambo, ya ce ma’aikatan sun tara kuɗaɗen ne domin nuna goyon baya ga takarar Gwamna da kuma nuna godiya kan irin gudunmawar da ya bayar wajen inganta rayuwar ma’aikata da iyalansu.
A cewarsa, sama da ma’aikata 1,500 da ke aiki a KEDCO a halin yanzu sun samu aikin ne a zamanin Dokta Jamilu Gwamna.
Ya ce baya ga kuɗaɗen da aka tara, ma’aikatan za su samar da kayayyakin yaƙin neman zaɓe da suka haɗa da allunan talla, fastoci, rigunan T-shirt da kuma yi wa motocin kamfen kwalliya domin ƙara wa takararsa ƙarfi.
Sambo ya kuma bayyana cewa suna shirin kafa cibiyoyin sa ido kan zaɓe a faɗin jihar domin wayar da kan jama’a da kuma bibiyar harkokin zaɓe gabanin zaɓen gwamna.
“Muna mara wa Dokta Jamilu Gwamna baya ne saboda mun ga yadda ya taimaka wajen canza rayuwar mutane da dama. Ya ba mutane damar samun abin dogaro da kai da kuma kula da iyalansu. Wannan ita ce hanyarmu ta nuna godiya ga irin alherin da ya yi mana,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa ma’aikatan sun ƙuduri aniyar ci gaba da wayar da kan jama’a domin ganin APC ta samu nasara a zaɓen gwamna mai zuwa.
Da yake mayar da martani, Dokta Jamilu Gwamna ya bayyana cewa wannan gagarumar goyon baya ta ba shi mamaki matuƙa, yana mai cewa bai taɓa tsammanin irin wannan karamci daga ma’aikatan ba.
“A yau zuciyata cike take da farin ciki. Ban taɓa tunanin cewa mutanen da muka taimaka musu za su haɗu wata rana su nuna mana irin wannan ƙauna da girmamawa ba. Idan ka taimaki mutane, ba ka yi hakan ne da niyyar samun wani abu a madadinsa ba. Amma abin da suka yi ya nuna cewa alheri ba ya ɓaci,” in ji shi.
Ya danganta wannan goyon baya da falalar Allah, yana mai cewa hakan ya nuna muhimmancin samar da ayyukan yi ga matasa da sauran al’umma domin su dogara da kansu.
Ɗan takarar na APC ya yi alƙawarin cewa idan aka zaɓe shi gwamna, samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arziki za su kasance daga cikin manyan manufofin gwamnatinsa.
Ya ce gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen samar wa matasa, mata da sauran marasa galihu damammakin tattalin arziki domin inganta rayuwarsu da kuma ƙarfafa ci gaban Jihar Gombe.
“Matasa su ne ƙashin bayan kowace al’umma. Idan suna da aikin yi, al’umma za ta samu zaman lafiya, ci gaba da bunƙasar tattalin arziki. Da yardar Allah, za mu ba samar da ayyukan yi muhimmanci domin gina makomar jihar mu,” in ji Gwamna.
