Katsina United ce za ta lashe gasar NPFI a kakar wasanni mai zuwa – Sarajo Abukur

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Ma’aikatar wasanni ta Jihar Katsina ta lashi takonin ganin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Katsina United ta lashe gasar (NPFL) da samun tikitin gasar nahiyar Afirka.

A lokacin taron masu ruwa da tsaki da ma’aikatan wasanni ta shirya tayi nazarin kakar wasannin da ta gabata da shirye-shiryen kakar wasa mai zuwa.

Kamar yadda sashin yaɗa labarai na ma’aikatar,ta umarci mahukuntan ƙungiyar ƙwallon ƙafar ta Katsina United da su tabbatar sun kawo kofin gasar firimiya ta Najeriya wato (NPFL) ko samo tikitin shiga gasar nahiyar Afirka a kakar wasa mai zuwa.

Kwamishinan wasannin jihar,Injiniya Surajo Yazeed Abukur, ne ya bayyana hakan yayin taron masu ruwa da tsaki da ya gudanar domin nazarin yadda kakar wasa ta 2025 zuwa 2026 ta gudana da kuma tsara dabarun kakar wasa mai zuwa.

Da yake jawabi ga mahalarta taron, kwamishinan ya bayyana cewa an shirya taron ne domin yin bitar yadda ƙungiyar ta taka rawar gani da ƙalubalen da ta fuskanta a kakar da ta gabata tare da tattara shawarwari da hanyoyin da za su taimaka wajen ƙara ƙarfafa ƙungiyar.

Injiniya Abukur ya ce duk da irin goyon bayan da gwamnatin jihar ke bai wa ƙungiyar akwai buƙatar ‘yan wasa,masu horaswa da jami’an ƙungiyar su ƙara himma da sadaukar da kai domin cimma burin da aka sanya a gaba.

Ya yabawa kwamitin riƙon ƙwarya na ƙungiyar bisa yadda suka jagoranci ƙungiyar ta kammala kakar wasa a matsayi na tara da maki 52,duk da kalubalen da ƙungiyar ta fuskanta na buga wasannin guda biyar a jihar Kwara.

Kwamishinan ya ce za a ɗauki matakan da suka dace domin hana sake faruwar irin wannan matsala tare da tsara hanyoyin da za su taimaka wajen ɗaukaka ƙungiyar zuwa matsayin da gwamnatin jihar ta sanya a gaba.

A nasa jawabin, shugaban riƙo na ƙungiyar,Alhaji Surajo Baba Malumfashi,ya nuna gamsuwarsa da matsayin da ƙungiyar ta kammala kakar wasan ta bana tare da tabbatar da cewa da goyon bayan ma’aikatar da sauran masu ruwa da tsaki a harkar ƙwallon ƙafa kungiyar za ta sake tsarawa domin cimma manufofin da aka gindaya.

Abukur ya sanar da cewa Katsina United ta buga wasanni 38 a kakar wasa ta 2025_26, inda ta yi nasara a wasanni 14, ta yi canjaras a wasanni 10, sannan ta sha kashi a wasanni 14.

Haka kuma ƙungiyar ta samu nasarori 12 a gida,ta yi canjaras 4, sannan ta yi rashin nasara sau 3. A wasannin waje kuwa, ta samu nasara sau 2, ta yi canjaras sau 6, sannan ta sha kashi sau 11.

Masu ruwa da tsakin da suka halarci taron sun yaba da rawar da kwamitin rikon ƙwarya na ƙungiyar ya taka tare da bayar da shawarwari da dabaru da za su taimaka wajen tabbatar da cimma burin da aka sanya wa ƙungiyar.

Haka kuma sun yabawa kwamishinan wasanni,Injiniya Surajo Yazeed Abukur, bisa shirya wannan muhimmin taro,wanda suka bayyana a matsayin abin da ya zo a kan lokaci kuma zai taimaka matuƙa wajen magance yawancin matsalolin da ƙungiyar ke fuskanta.

By ukarofi

Leave a Reply