Bassirou Faye na Senegal ya zama sabon shugaban ECOWAS

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

An zaɓi Shugaban ƙasar Senegal, Bassirou Faye a matsayin sabon shugaban Ƙungiyar Ƙasashe Masu ƙarfin Tattalin Arziƙi ta Afirka ta Yamma (ECOWAS), bayan gudanar da zaɓe a Birnin Freetown, lamarin da ke nuna cewa ya gaji Julius Maada Bio na ƙasar Sierra Leone a muƙamin.

Faye ya zama shugaban na ECOWAS ne a zaman da ƙungiyar ta saba gudanarwa da ya ƙunshi jagororin gwamnatocin shiyyar karo na 69 a ranar Lahadi.

Shugaban na Senegal ya maye gurbin Maada Bio ne da aka zaɓa a watan Yuni, 2025 a matsayin shugaban ƙungiyar bayan Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu ya kammala wa’adinsa na shekara biyu a jagorancin ECOWAS.

Ana sa ran Faye zai yi ƙoƙarin shawo kan ƙasashen Burkina Faso, Mali da Nijar zuwa cikin ƙungiyar bayan ficewarsu shekaru biyu da suka gabata, wajen buɗe ƙofar tattaunawa da su.

Haka kuma, an naɗa Biram Diop a matsayin shugaban Hukumar ECOWAS, lamarin da ba shi damar maye gurbin Dakta Omar Touray.

By Babaji