An samu ɗimbin cigaba a ƙarƙashin APC – cewar Bello

Daga BASHIR ISAH

Ministan Abuja Malam Muhammad Musa Bello ya ce, gwamnatin jam’iyyar APC ta samar da cigaba masu yawa tun bayan kama mulki a 2015.

Bello ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin kwamitin shirin sabunta rijistar mambobin APC na Abuja a Alhamis da ta gabata.

Yana mai cewa, “Waɗanda suke mazauna Abuja, ko masu yawan ziyartar ta a 2015, sun san akwai bambanci da Abuja ta wancan lokaci da ta yanzu.”

Daga nan, Bello ya nuna gamsuwarsa dangane da naɗa Hon. Sanda Umar Garba da aka yi a matsayin Shugaban Kwamitin Kula da Shirin Sabunta Rijistar ‘Ya’yan APC na Abuja. Tare da bayyana shi a matsayin mai ƙwazo.

Haka nan, Ministan ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga kwamitin da yin aiki tukuru wajen wayar da kan jama’ar Abuja don a fito a yi rijista. Kana ya shaida wa kwamitin samun cikakken haɗin kan Hkumar Abuja.

Tun farko da yake jawabi, Shugaban Kwamitin, Hon Garba, ya nuna farin cikinsa da turo su Abuja da aka yi don yin aikinsu. Tare da cewa, Abuja wuri ne mai lumana da zai ba su damar gudanar da aikinsu cikin sukuni.

Duka waɗannan bayanai na ƙunshe ne cikin takardar bayani wadda ta fito ta hannun Babban Sakataren Yaɗa Larabai na Hukumar Abuja, Mr Anthony Ogunleye, a Alhamis da ta gabata.