Mun shirya wa yin zaɓen cike gurbi a Neja, cewar INEC da ‘yan sanda

Daga WAKILIN MU

Kwamishinan Zaɓe mai zama a Jihar Neja (REC), Farfesa Samuel Egwu, ya ce Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta gama shiryawa tsaf domin gudanar da zaɓen cike gurbi da za a yi a Mazaɓar Tarayya ta Magama/Rijau da ke jihar a ranar Asabar, 6 ga Fabrairu, 2021.

Egwu ya faɗi haka ne a ranar Alhamis lokacin da ya ke tattaunawa da wakilin Hukumar Dillancin Labarai ta Nijeriya (NAN) a Minna.

Ya ce hukumar sa ta gama duk wani shirin yin zaɓe mai inganci da tsare gaskiya, domin kuwa ta horas da ma’aikatan zaɓe mutum 1,258 saboda zaɓen. 
 
Ya ƙara da cewa masu zaɓe da aka yi wa rajista mutum 159,347 za su kaɗa ƙuri’ar su a rumfunan zaɓe 307, kuma har masu zaɓe guda 158,624 sun karɓi katin su na zaɓe na dindindin.

Egwu, wanda ya ce har hukumar tasa ta gama rarraba kayan da za a yi aiki da su a zaɓen, ya bayyana cewa ya na da tabbacin za a gudanar da zaɓen cikin nasara.
 
Ya ce: “Mun gama shirya ma’aikatan mu tare da ba su horo kan sanin makamar aiki ta yadda za su gudanar da zaɓen cikin inganci da tsare gaskiya idan ranar 6 ga Fabrairu ta zo.”

Shi ma Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Neja ya bada tabbacin cewa sun gama duk wani shiri na bada tsaro a lokacin zaɓen ciken gurbin.

Kwamishinan, Alhaji Adamu Usman, ya faɗi haka ne a lokacin zantawar sa da Hukumar Dillancin Labarai ta Nijeriya (NAN) a Minna a ranar Alhamis.

Usman ya ce ‘yan sanda tare da sauran hukumomin tsaro da ke jihar su na aiki tare don tabbatar da an yi zaɓen ba tare da wata hatsaniya ba.
 
Ya ce: “Mun tura isassun ma’aikata masu ɗauke da makamai domin inganta yanayin siyasa kafin da lokacin da kuma bayan zaɓen.

“Ina bada tabbaci ɗari bisa ɗari ga duk mazauna wannan mazaɓar masu son bin doka da oda cewa za su iya zuwa su kaɗa ƙuri’un su a ranar 6 ga Fabrairu ba tare da fargabar barazana ga rayukan su ko dukiyoyin su ba.”