Siyasa

Gwamna Bello ya naɗa sabon shugaban ma’aikata

Gwamna Bello ya naɗa sabon shugaban ma’aikata

Daga FATUHU MUSTAPHA Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya naɗa Mrs. Hannah Odiyo a matsayin sabuwar Shugaban Ma'aikata na Gwamnatin Jihar. Sakataren Gwamnatin Jihar, Dr. Folashade Arike Ayoade ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis. Kafin naɗin nata, Mrs. Odiyouta ta kasance riƙe da matsayin sakatariyar Ma'aikatar Harkokin Noma na Jihar Kogi. Gwamna Bello ya yi yabo na musamman ga shugabar ma'aikata mai barin gado, Deborah Ogunmola dangane da irin gudunmawar da ta bayar ga cigaban sha'anin aikin gwamanti a jihar. Kana ya taya sabuwar shugabar murnar samun sabon muƙami tare da…
Read More
Fintiri ya ƙaddamar da hanyoyi a Adamawa

Fintiri ya ƙaddamar da hanyoyi a Adamawa

Daga BASHIR ISAH Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya ƙaddamar da hanyoyi na sama da kilomita 340 a sassan jihar da zimmar sauƙaƙa wa 'yan karkara sha'anin zirga-zirga Aikin samar da hanyoyin haɗin guiwa ne tsakanin gwamnatin Adamawa da Bankin Duniya da cibiyar French Development Agency ƙarkarshin Shirin Samar wa Karkara Hanyoyi na Gwamnatin Tarayya (RAMP-2). Hanyoyin da aka aka ƙaddamar sun shafi ƙananan hukumomi 21 da jihar ke da su ne. Yayin da yake magana a wajen ƙaddamar da hanyoyin, Gwamna Fintiri ya ce gwamnatinsa ba ta sa wasa ba wajen biyan kasonta ga shirin haɗin guiwar wanda…
Read More
Yawan masu zaɓe a Nijeriya ya tsaya tsakanin kashi 30 zuwa 35 cikin ɗari – inji INEC

Yawan masu zaɓe a Nijeriya ya tsaya tsakanin kashi 30 zuwa 35 cikin ɗari – inji INEC

Daga WAKILIN MU Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa yawan masu zaɓe a Nijeriya bai fi kashi 30 zuwa 35 cikin ɗari na waɗanda su ka yi rajista a zagaye biyu na zaɓuɓɓukan da aka yi na baya-bayan nan ba. Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka a wajen taron tuntuɓa na farko da hukumar ta shirya tare da ƙungiyoyi masu zaman kan su (CSOs) na shekarar 2021 wanda aka yi a ranar Talata a Abuja. Yakubu ya ce a yayin da wasu zaɓuɓɓukan sun fi samu yawan fitowar masu zaɓe, a wasu kuma ba…
Read More
Zan taimaki Nijeriya wajen yaƙi da matsalolin tsaro muddin na lashe zaɓe – inji Bazoum

Zan taimaki Nijeriya wajen yaƙi da matsalolin tsaro muddin na lashe zaɓe – inji Bazoum

Daga WAKILIN MU A makon da ya gabata ne ɗan takarar Shugaban Ƙasar Nijar ƙarkashin jam'iyyar PNDS Tarayya, Alhaji Mohammed Bazoum, ya kai wa Shugaba Muhammadu Buhari ziyara ta musamman a Daura domin neman goyon bayansa. Yayin ziyarar, Buhari da Bazoum sun tattauna muhimman batutuwa ciki har da batun takarar Bazoum da batun kwararar ɓatagari daga Nijar zuwa Nijeriya da kuma akasin haka. Haka nan tattaunawar tasu ta taɓo batun matsalolin tsaron da Nijeriya ke fama da su da zimmar Bazoum zai taimaka wa Buhari wajen yaƙi da matsalolin idan ya lashe zaɓe mai zuwa. Bazoum bai bar Nijeriya ba…
Read More
Ambaliya: Ɗan Majalisa ya shige wa mazaɓarsa gaba wajen samun tallafi

Ambaliya: Ɗan Majalisa ya shige wa mazaɓarsa gaba wajen samun tallafi

Daga WAKILIN MU Ɗan Majalisar Wakilai ta Ƙasa Hon. Nicholas Ossai na jam'iyyar PDP daga jihar Delta, ya yi sanadin rabon tallafin kayayyaki da dama da kuɗinsu ya kai Naira miliyan 30 ga jama'ar da ambaliya ta shafa gundumar Ndokwa/Ukwuani da ke jihar. Hon. Ossai ya ce Hukumar Bada Gajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ce ta bada tallafin da aka rabar wa waɗanda lamarin ya shafa. A bayanin da ya yi Lahadin da ta gabata, ɗan majalisar ya ce kayayyakin tallafin da aka rabar sun haɗa da kwanon rufi, ƙusoshi, silin, siminti, katifu, hidan sauro, barguna, kayan abinci da dai…
Read More
2023: Ba za mu zaɓi matsafa ba a Akwai Ibom – Mbang

2023: Ba za mu zaɓi matsafa ba a Akwai Ibom – Mbang

Daga WAKILIN MU Tsohon Shugaban Ƙungiyar Kiristoci ta Ƙasa (CAN) Sunday Mbang, ya gargaɗi 'yan siyasar jihar Akwa Ibom masu neman tsayawa takara a zaɓuɓɓukan 2023 da su nesanta kansu da harkokin ƙungiyar asiri. Mbang ya yi wannan gargaɗi ne sa'ilin da yake amsa tambayoyin manema labarai a wajen taron addu'a ta musamman da aka shirya wa 'yan majalisun tarayya daga jihar don nema musu kariya daga cutar korona a ƙarshen mako a Uyo, babban birnin jihar. Jagoran addinin ya ce Allah ba zai bari duk wani ɗan siyasa a jihar mai mu'amala da tsafi da makamancin haka ya zama…
Read More
INEC za ta samar da sabbin mazaɓu a faɗin Nijeriya kafin zaɓen 2023 – Mahmood Yakubu

INEC za ta samar da sabbin mazaɓu a faɗin Nijeriya kafin zaɓen 2023 – Mahmood Yakubu

Daga WAKILIN MU Nan da lokacin da za a gudanar da babban zaɓe a Nijeriya, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) za ta samar da ƙarin mazaɓu a faɗin ƙasar. Shugaban kwamitin wayar da kan masu zaɓe a hukumar (IVEC), Mista Festus Okoye, shi ne ya bayyana haka a Abuja. Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, a cikin Agustan 2014 INEC ta gabatar da buƙatar samar da ƙarin mazaɓu 30,027, inda arewacin ƙasar za ta samu mazaɓu 21,615 yayin da kudu za ta samu 8,412. Wannan ya janyo ce-ce-ku-cen da ya sa INEC ta watsar da shirin. Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ya…
Read More
Mun shirya wa yin zaɓen cike gurbi a Neja, cewar INEC da ‘yan sanda

Mun shirya wa yin zaɓen cike gurbi a Neja, cewar INEC da ‘yan sanda

Daga WAKILIN MU Kwamishinan Zaɓe mai zama a Jihar Neja (REC), Farfesa Samuel Egwu, ya ce Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta gama shiryawa tsaf domin gudanar da zaɓen cike gurbi da za a yi a Mazaɓar Tarayya ta Magama/Rijau da ke jihar a ranar Asabar, 6 ga Fabrairu, 2021. Egwu ya faɗi haka ne a ranar Alhamis lokacin da ya ke tattaunawa da wakilin Hukumar Dillancin Labarai ta Nijeriya (NAN) a Minna. Ya ce hukumar sa ta gama duk wani shirin yin zaɓe mai inganci da tsare gaskiya, domin kuwa ta horas da ma'aikatan zaɓe mutum 1,258 saboda zaɓen.  Ya…
Read More
An samu ɗimbin cigaba a ƙarƙashin APC – cewar Bello

An samu ɗimbin cigaba a ƙarƙashin APC – cewar Bello

Daga BASHIR ISAH Ministan Abuja Malam Muhammad Musa Bello ya ce, gwamnatin jam'iyyar APC ta samar da cigaba masu yawa tun bayan kama mulki a 2015. Bello ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin kwamitin shirin sabunta rijistar mambobin APC na Abuja a Alhamis da ta gabata. Yana mai cewa, "Waɗanda suke mazauna Abuja, ko masu yawan ziyartar ta a 2015, sun san akwai bambanci da Abuja ta wancan lokaci da ta yanzu." Daga nan, Bello ya nuna gamsuwarsa dangane da naɗa Hon. Sanda Umar Garba da aka yi a matsayin Shugaban Kwamitin Kula da Shirin Sabunta…
Read More
Buhari ya sabunta rijistarsa ta zama a APC

Buhari ya sabunta rijistarsa ta zama a APC

Daga FATUHU MUSTAPHA A ranar Asabar da ta gabata Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sabunta rijistarsa ta zama cikakken dan jam'iyyarsu ta APC, a mahaifarsa Daura da ke jihar Katsina. Tare da kira ga daukacin shugabannin jam'iyyar da karfafa kwazo wajen tabbatar da APC ta samu karin tagomashi a matakin farko. Buhari ya yi wannan kira ne a lokacin da ya karbi bakuncin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan da wasu gwamnoni hada da wasu 'ya'yan jam'iyyar APC a garin Daura, jim kadan bayan ya kammala sabunta rijistarsa ta jam'iyya a Gundumar Sarkin Yara. A wata sanarwa da mai magana…
Read More