01
Mar
Daga FATUHU MUSTAPHA Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa za ta shirya wata bita ta musamman domin wayar da kan ma'aikatan ta na sashen faɗakar da masu zaɓe da ke hedikwatar ta da kuma jihohi. Wata sanarwa da ta fito daga hukumar a ranar Asabar ta ce bitar, mai taken "Faɗakar da Mai Faɗakarwa", wato "Train-the- Trainers (ToT)", an kasa ta zuwa gida biyu saboda matsalar annobar korona (COVID-19) da ake fama da ita. Kashin farko za a yi bitar ga shugabannin sashen faɗakar da masu zaɓe (HODs VEP) da ke jihohin Kudu da kuma waɗanda su ke…