Zamfara: Wani jigon APC ya musanta zancen yana da matsala da EFCC

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Wani  mai ruwa da tsaki kuma tsohon ɗan takarar gwamna a Zamfara yayin zaɓen 2019, Hon. Aminu Sani Jaji ya ce bai san da wata shari’a da ta haɗa shi da hukumar Hana Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ba har ta kai ga sanya masa alama a gidansa da ke Gusau ranar Juma’a.

Ɗan siyasar wanda ya yi magana da ’yan jaridu a wayar tarho ya ce, babu wanda ya gayyace shi ko ya kusanta shi ko dai a EFCC ko kuma a ko wace hukuma, kuma saboda haka ya zama abin mamaki a gare shi yadda ya wayi gari ya ga gidansa da ake zargin cewa hukumar EFCC ta sanya alama a Gusau babban birnin jihar.

Jaji ya ƙara da cewa, “Babu abin da ba zai yiwu ba, amma a iyakar sanina ba ni da wata ƙara da kowa, kuma ko da wani ya rubuta koke a kaina ya kamata a gayyace ni don amsa tambayoyi amma ina shakkar idan wannan matakin daga EFCC ne.”

Ya yi kira ga magoya bayansa da su kwantar da hankula yayin da ake gudanar da bincike kan lamarin.

Ya kuma gode wa abokai, abokan siyasa da masu yi masa fatan alheri kan damuwar da suka nuna masa, yana mai cewa za a gano bakin zaren kuma a magance ta yadda ya kamata.