Masu Umura daga Nijeriya sun isa Saudiya

Daga WAKILIN MU

An samu ƙarin ‘yan Nijeriya su 23 suka bar gida zuwa ƙasa mai tsarki a Alhamis da ta gabata domin gabatar da aikin Umura.

Maniyatan sun tashi ne ta babban filin jirgin saman Murtala da ke Legas zuwa babban filin jiragin sama na Sarki Abdul Aziz da ke Jeddah. Saudi Arabia.
 
HAJJ REPOTERS ta ruwaito cewa kamfanonin New Crescent International Travels da kuma Rhoudah Travel sun taimaka wajen tsara tafiyar maniyatan zuwa ƙasa mai tsarki.

Ethiopian airline mai lamba ET 2402 shi ne jirgin da ya yi jigilar maniyatan inda suka isa Saudiya bayan shafe sa’o’i biyar a sararin samaniya.
 
Daraktan kamfanin Raudah Travels And Tours Ltd, Alh Umar Abdulhadi Alfuti, ya shaida wa HAJJ REPORTERS kamfaninsa da na New Crescent Tour sun kammala dukkan shirye-shirye, inda suke sa ran jigilar baki ɗayan maniyatan a ranar 18 ga Fabrairu zuwa ƙasa mai tsarki.