Allah Ya yi wa Dikko rasuwa

Allah Ya yi wa tsohon Shugaban Hukumar Yaƙi da Fasa-ƙwauri ta Nijeriya, Abdullahi Dikko Inde, rasuwa a ranar Alhamis (18/02/2021).

Iyalan marigayin ne suka bada bayanin tabbacin rasuwarsa.

Sanarwar da ta fito daga hannun Mai Magana da Yawun Hukumar Kwastam na Ƙasa, DC Joseph Attah, ta nuna za a gudanar da jana’izar marigayin a ranar Juma’a (19/02/2021), bayan sallar Juma’a a babban masallacin ƙasa da ke Abuja.

A halin rayuwarsa, marigayin ya shugabanci Hukumar Kwastam daga 2009 zuwa 2015.

Attah ya yi fatan Allah Ya bai wa iyalan marigayin danganar wannan rashi, tare da fatan Allah Ya sa Aljanna ta zamanto makomarsa.