Ganduje ya rantsar da sabbin ciyamomi a Kano

Daga AISHA ASAS

Gwamnatin Jihar Kano ta rantsar da sabbin zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomin jihar su 44 a Juma’ar da ta gabata.

Sa’ilin da yake jawabi yayin bikin rantsarwar, Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya ce cika aiki shi ne babban abin da gwamnatinsa ta fi maida hankali a kai. Tare da kira a gare su da su kasance masu ƙwazo da kuma yin aiki da gaskiya.

A cewar gwamnan, ƙanan hukumomi a matsayin mataki na uku na tsarin gwamnati na buƙatar jajirtattun shugabanni da za su yi aiki tukuru.

Yana mai cewa sadaukarwa da kuma cika aiki su ne shugabannin ke buƙata domin samun aiwatar da ayyukan da al’umma za ta yaba musu.

Ganduje ya ja hankalin ciyamomin da su maida hankali wajen aiwatar da ayyukan da jama’a za su amfana da su, kamar kula da fannin kiwon lafiya da ƙirƙiro da ayyuka ta hanyar koyar da sana’o’i da gina hanyoyi da sauransu.