Zaɓen ƙananan hukumomin Oyo ɓata kuɗi da lokaci ne, inji APC

Daga FATUHU MUSTAPHA

Jam’iyyar APC a jihar Oyo, ta ce zaɓen ƙananan hukumomi da aka shirya sake gudanarwa a ranar 15 ga Mayu mai zuwa a jihar, tamkar ɓata kuɗi da kuma lokaci ne.

Shugaban riƙo na APC a jihar, Chief Akin Oke, ya bayyana zaɓen a matsayin lamarin da ba zai yi armashi ba balle ya ja hankalin ‘yan siyasa na gaskiya.

Yana mai cewa, an ga faruwar irin haka a baya, inda gwamnan jihar kan haifar da tsaiko ga sha’anin ƙananan hukumomin jihar waɗanda su ne mataki na uku a matakan gwamnati.

Oke, ya ce zai kasance abu mafi muni ga Gwamna Makinde yayin da kotu ta buƙaci ya biya diyya ga waɗanda ya ɓata musu lokaci na tsawon shekaru biyu ba tare da ya yi abin da ya kamata ba.

Yana mai cewa wannan karon, Makinde da jam’iyyarsa za su ji kunya saboda a bayyane yake cewa tsare-tsarensa sun saɓa wa doka.