Shugaban jaridun Manhaja da Blueprint ya sabunta rajistarsa a APC

Daga FATUHU MUSTAPHA

A Juma’ar da ta gabata Shugaban Jaridun Manhaja da Blueprint, Alhaji Mohammed Idris Malagi, ya sabunta rajistarsa ta zama ɗan jam’iyyar APC a rumfar zaɓensa da ke Malagi, a ƙaramar hukumar Gbako da ke jihar Neja.

Bayan kammala rajistarsa, Alhaji Idris ya yaba da yadda aikin yin rajistar ke guna cikin lumana a rumfar zaɓensu, tare da kira ga ‘yan jam’iyyarsu ta APC a faɗin jihar kan kowa ya tabbatar da ya yi rajista ko sabunta rajistarsa.

Yana mai cewa, “Na yi matuƙar farin ciki da yadda aikin yin rajistar ke gudana. Wannan wata alama ce mai nuna yadda ‘yan jam’iyyar da ma masu sha’awar shigan ta ke da burin bunƙasa jam’iyyar da ma dimukraɗiyyar jihar.

“Don haka nake kira ga ɗaukacin ‘ya’yan jam’iyyar da ma masu sha’awar su shige ta a jihar da cewa kowa ya je ya yi rajista.”

Alhaji Idris wanda har wa yau, shi ne shugaban kamfanin Bifocal Group da WeFM da ke Abuja, ya ce ya yi koyi ne da Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamnan Neja, Alhaji Abubakar Sani-Bello haɗa da shugabannin APC na ciki da wajen Neja waɗanda suka riga suka yi tasu rajistar a wurare daban-daban, wajen sabunta rajistarsa.

Daga nan ya yi kira ga al’ummar jihar Neja da su riƙa shiga ana harkoki da su a matakin jiha da ƙasa maimakon zama ‘yan kallo.

Ta bakinsa, “Wajibi ne mu haɗa hannu wajen ciyar da dimukraɗiyyar Nijeriya gaba mu gina al’ummominmu, jiharmu da ma ƙasa baki ɗaya ta hanyar shiga ana damawa da mu amma ba mu zama ‘yan a bi yarima a sha kiɗa ba.

Jigon ya yaba wa Shugaba Buhari da kuma Gwamna Sani Bello bisa yadda suka sakar wa kowa mara don tsoffi da sabbin ‘yan jam’iyyar kowa ya yi rajistarsa ba tare da wata takura ba.

Daga bisani ya shawarci jama’a da a kiyaye dukkan dokokin yaƙi da cutar korona da aka shimfiɗa yayin yin rajistar domin taimaka wa ƙoƙarin gwamnati wajen yaƙi da cutar.

A ƙarshe Alhaji Idris Malagi, ya yi godiya ga dukkan waɗanda suka yi masa rakiya zuwa wajen sabunta rajistarsa. Shugabannin APC na yankin da abokan hulɗa da magoya baya na daga cikin waɗanda suka yi masa rakiyar.