30
Mar
Daga AISHA ASAS Jam'iyar PDP a Jihar Neja ta bayyana dakatar da Tsohon Gwamnan Jihar Neja, Dakta Mu'azu Babangida Aliyu. PDP ta Ƙaramar Hukumar Chanchaga ta dagatar da Aliyu ne bisa wasu zarge-zarge a kansa ciki har da haifar da rashin jituwa a tsakanin shugabannin jam'iyyar. Kazalika, an zargi Tsohon Gwamnan da yi wa jam'iyya zagon-ƙasa, sai batun rashin martaba faɗar Gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai, wanda ya buƙaci a haɗu a gudanar da babban taron jam'iyya na jiha. Haka nan, akwai zargin cewa Dr Mu'azu Babangida Aliyu ya tallafa wa APC da kuɗi Naira milyan N450 yayin zaɓen…