Daga AISHA ASAS
Jam’iyar PDP a Jihar Neja ta bayyana dakatar da Tsohon Gwamnan Jihar Neja, Dakta Mu’azu Babangida Aliyu.
PDP ta Ƙaramar Hukumar Chanchaga ta dagatar da Aliyu ne bisa wasu zarge-zarge a kansa ciki har da haifar da rashin jituwa a tsakanin shugabannin jam’iyyar.
Kazalika, an zargi Tsohon Gwamnan da yi wa jam’iyya zagon-ƙasa, sai batun rashin martaba faɗar Gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai, wanda ya buƙaci a haɗu a gudanar da babban taron jam’iyya na jiha.
Haka nan, akwai zargin cewa Dr Mu’azu Babangida Aliyu ya tallafa wa APC da kuɗi Naira milyan N450 yayin zaɓen 2015 wanda hakan ya taimaka wa APC wajen samun galaba a kan jam’iyyarsa PDP.
Sai kuma zargin rashin shiga harkokin jam’iyya da haifar da rarrabuwar kawunan mambobin jam’iyya da sauransu.
Takwas daga cikin shugabannin gundumomi goma na PDP da ake da su a Ƙaramar Hukumar Chanchaga su ne suka sanya hannu a takardar dakatarwar da aka yi wa Babangida Aliyu. Tare da neman amsarsa kan zarge-zargen da aka yi masa tsakanin makonni biyu daga ranar da aka ɗauki matakin dakatarwar.
