Filato: Gobara ta yi ta’asa a kasuwar doya a Qu’an Pan

Daga WAKILINMU

An samu aukuwar mummunar gobara a kasuwar doya ta Namu ta Tsakiya da ke yankin Ƙaramar Hukumar Qu’an Pan, Jihar Filato.

Manhaja ta kalto cewa gobarar ta auku ne da daddare a Lahadin da ta gabata inda ta lalata tarin doya da sauran kayayyakin abincin na muƙudan kuɗaɗe.

Sai dai ya zuwa haɗa wannan labari, jaridar Daily Nigerian ta ce ba a kai ga gano sababin faruwar gobarar ba.

Bayanai daga yankin sun nuna sama da manona 100 ne ibtila’in gobarar ya shafa. Tare da yin kira ga gwamnati a matakai daban-daban da su tallafa wa waɗanda lamarin ya shafa domin samun sassaucin hasarar da suka tafka.

Tuni dai Sanata mai wakiltar shiyyar Filato ta Kudu, Nora Dadu’ut, ya jajanta wa manoman da ma sarkin yankin, Safiyanu Allahnana, bisa aukuwar gobarar.

Shi ma Sanata Dadu’ut, ya yi kira ga gwamnati da ma ‘yan Nijeriya da a duba a agaza wa waɗanda ibtila’in ya shafa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *