NAFDAC ta gargaɗi ‘yan Nijeriya kan amfani da jabun shayi

Daga WAKILINMU

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna (NAFDAC), ta yi jan hankali ga ‘yan Najeriya game da wani jabun shayi da ake sayarwa wanda aka ce yana maganin ciwon sukari.

Hukumar ta gargaɗi ‘yan nijeriya da su guji yin amfani da ‘insulin tea’ wanda ko rajista bai da shi balle kuma ingancin warkar da wata cuta.

Shugabar NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye ce ta yi wannan gargaɗi a wata sanarwar manema labarai da ta fitar a Lahadin da ta gabata a Abuja.

Adeyeye ta buƙaci duk inda aka ga ana sayar da wannan shayi na ‘insulin tea’ a gaggauta sanar da ofishin NAFDAC mafi kusa.

Ta ce domin kwarmata wa hukumar batun shayin ana iya kiran waya ta waɗannan lambobi a kowane layi kuma kyauta, wato 20543, ko kuma a yi hakan ta ziyartar shafin intanet na hukumar.