APC za ta shafe shekara 32 riƙe da mulkin ƙasa, cewar Buni

Daga WAKILINMU

Shugaban Kwamitin Riƙo na Ƙasa na Jam’iyyar APC kuma Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya ce jam’iyyarsu na da niyar yin mulkin ƙasa nan da shekaru 32 masu zuwa.

Buni ya bayyana haka ne a wajen taron ƙaddamar da wani kwamitin APC na musamman mai mambobi 61, ƙarƙashin shugabancin Gwamnan Jigawa Badaru Abubakar, tare da ɗora wa kwamitin nauyin fito da hanyoyin da za a bi wajen gyara zaman jam’iyyar tasu.

Kazalika, Buni ya ce ana buƙatar kwamitin ya gudanar bincike a tsakanin mambobin jam’iyya da ma al’umma baki ɗaya sannan ya fitar da manufa da burin da ake son cim ma tare da samar da tsare-tsaren da shawarwarin da za su taimaka wajen ƙarfafa haɗin kan ‘yan jam’iyya a faɗin kasa.

Don haka ya ce, “an kafa kwamitin ne don ya zama tamkar wani ginshiƙi ga cigaban da muke samarwa don gina jam’iyya mai ƙarƙo da za ta iya tafiya daidai da kowane zamani.

“Burinmu shi ne samar da damar da za ta bai wa jam’iyyarmu ikon yin mulki wuce wa’adi na 6, na 7 har ma da na 8 a kan mulki, inda za mu aiwatar da ayyukan da za su taɓa rayuwar ‘yan Nijeriya ya zamana kuma babu wata jam’iyya da ta sha gaban APC.”

Da yake jawabi a madadin ‘yan kwamitin jim kaɗan bayan ƙaddamarwar, Shugaban Kwamitin kuma Gwamnan Jihar Jigawa, Badaru Abubakar, ya ce kulli yaumi ana samun ‘yan Nijeriya da dama da ke komawa APC, kuma aikin rajistan zama ɗan jam’iyya da ke kan gudana ya nuna irin tagomashin da jam’iyyar ta samu a ƙasa.

Badaru ya bai wa shugabannin jam’yyarsu tabbacin cewa kwamitin zai yi aiki kamar yadda aka buƙace shi domin taimaka wa jam’iyyar wajen cim ma tsare-tsarenta.