Attah ya yi ƙarin haske kan batun biyan harajin sayen jiragen sama

Daga AISHA ASAS

Hukumar Yaƙi da Fasa-ƙwauri ta Ƙasa ta yi ƙarin haske tare da kore raɗe-raɗin da aka yi ta yaɗawa kan batun biyan harajin VAT da Kwastam Duti kan sayen jiragen sama da sauran kayayyakin jiragen.

Idan dai za a iya tunawa, wasu kafafen yaɗa labarai sun ruwaito Shugaban Air Peace Airline na cewa har yanzu Hukumar Kwastam na karɓar harjin Duti da na VAT duk da umarnin hani ga hakan da Gwamnatin Tarayya ta gindaya wanda a cewarsa hakan na maida wa kamfanonin sufurin jiragen sama hannun agogo a baya.

Sai dai mai magana da yawun hukumar na ƙasa, Joseph Attah, ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar cewa wannan batu ba gaskiya ba ne. Yana mai cewa, an kitsa haka ne don kawai a shafa wa hukumar baƙin fenti.

Attah ya ce, “Domin kawar da shakku kan lamarin, muna jan hankalinsa zuwa ga sashe na 39 na Dokar Kuɗi wadda aka gyara da ya ce, “Jiragen sama da aka yi wa rajista a Nijeriya kuma suke hada-hadar sufuri, an ɗauke musu biyan haraji yayin shigo da jirage, injinan jirgi da sauran kayayyakin jirage.” Dokar ba ta ɗage biyan abin da ya shafi CISS da ETLS ba, ɗagewar harajin Kwastam Duti da VAT kawai ta shafa.”

Attah ya ƙara da cewa, hukumarsu ba ta karɓi harajin Duti da VAT ba daga hannun kamfanin Air Peace wajen shigo da jirgin E195-E2 mai lambar rajista 5N-BYE, amma ta taƙaita kanta wajen karɓar abin da ya shafi ETLS CISS wanda ya kama N189,000,000.

Jami’in ya shawarci masu harkar jiragen sama su zamo masu mu’amala da hukumomin da suka dace tare da gudanar da harkokinsu daidai da ƙa’idojin da gwamnati ta shimfiɗa.