Kotu ta ɗaure Farfesa kan maguɗin zaɓe a Akwa-Ibom

Daga UMAR M. GOMBE

Wata babbar kotu a jihar Akwa-Ibom ta yanke wa Farfesa Peter Ogban hukuncin zaman kaso na shekara uku bayan da ta kama shi da laifin tafka maguɗin zaɓe.

Kotu ta kama malamin da laifin shirya sakamakon zaɓe na ƙarya tare da sanar da sakamakon yayin babban zaɓen 2019 a matsayinsa na shugaban zaɓe a shiyyar Akwa-Ibom ta Arewa maso-yamma.

Farfesan wanda malami ne a Jami’ar Calabar a Sashen Nazarin Harkokin Noma, ya tafka maguɗi wajen haɗa sakamon wasu ƙananan hukumomi guda biyu a wancan lokaci, wato ƙaramar hukumar Oruk Anam da Etim Ekpo.

A can baya, Mr Ogban ya shaida wa kotun yadda aka yi muna-muna wajen shirya sakamakon zaɓe don bai wa jam’iyyar APC damar samun galaba a kan abokiyar hamayyarta PDP.

Bayanai sun nuna an yi maguɗin ƙarin ƙuri’u guda 5,000 cikin ƙuri’un da APC ta samu a yankin Oruk Anam a lokacin zaɓen.

A wancan lokaci, Ministan Harkokin Yankin Niger Delta, Godswill Akpabio, shi ne ɗan takarar APC wanda ke son komawa majalisar dattawa a matsayin sanata bayan ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC.

Sai dai ɗan takarar PDP Chris Ekpenyong kuma tsohon Mataimakin Gwamnan Akwa Ibom State, ya doke Mr Akpabio a zaɓen da a ƙarshe aka samu hatsaniya.

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa Mai Zaman Kanta (INEC), ita ce ta gurfanar da Farfesa Ogban, inda bayan samun sa da aikata laifin da aka tuhume shi da aikatawa sai kotu ta yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekara uku da kuma tarar N100,000.

Bayan da Manhaja ta tattara sun nuna duk da dai Farfesan ya roƙi kotu da ta tausaya ta yi masa sassauci game da hukuncin da aka yanke masa, sai dai alkalin kotun, Augustine Odokwo, ya ce babu wani abu da za a iya yi face a bar doka ta yi aikinta kawai.