Ilimin ‘ya mace ya fi na namiji muhimmanci – Saratu Garba

Saratu Garba

Hajiya Saratu G. Abdul ƙwararriyar malamar jinya ce kuma babbar ɗaliba wadda ta zage damtse a ɓangaren karatun aikin jinya tun a nan gida Nijeriya har zuwa ƙasashen ƙetare. A yanzu haka ta na ƙasar Amurka ta na ci gaba da karatun digiri na uku a ɓangaren aikin jinya. Saratu Garba Abdullahi dai ta na sahun farko kuma gaba-gaba a rukunin matan da su ka samu ilimi mai zurfi a arewacin Nijeriya, musamman ma a ɓangaren aikin jinya da ta ke cigaba da neman ilimi da ƙwarewa a kai. An dai ce waƙa a bakin mai ita ta fi daɗi. Ga dai yadda hirar jaridar Manhaja da Saratu Garba Abdullahi ta kasance:

Daga AISHA ASAS a Abuja

Masu karatu za su so jin tarihin ki.
Suna na Saratu Garba Abdullahi. An haife ni a garin Birnin Kudu da ke Jihar Jigawa a Nijeriya. Na yi makarantar firamare a garin Birnin Kudu, sai kuma na tafi makarantar ‘yan mata ta haɗaka da ta ke Gwaram, duk dai a Jihar Jigawa. Bayan na gama sai na shiga makarantar koyon aikin jinya, wato ‘School of Nursing’, a garin Birnin Kudu. Daga nan sai na yi aiki na kusan shekara ɗaya a asibitin Haɗejiya, daga bisani na tafi makarantar koyon aikin ungozoma, wato ‘School of Midwifery’, da ke Kano. Bayan na gama sai na koma asibitin Haɗejiya na ci gaba da aiki a ɗakin karɓar haihuwa. Bayan na yi aiki na wani lokaci sai na tafi cibiyar yoyon fitsari da ke Katsina, wato ‘National Fistula Centre’, inda na koyi aikin kula da masu lalurar yoyon fitsari da bahaya. Bayan na gama na dawo, sai aka tura ni cibiyar yoyon fitsari ta Jihar Jigawa da ke garin Jahun. Bayan na yi aiki na wani lokaci sai na fara zuwa makarantar kiwon lafiya, wato ‘School of Health and Technology’, Jahun, ina koyarwa a matsayin ‘volunteer’. Daga baya sai na yanke shawarar na je na ƙaro karatu domin na ƙware a kan harkar koyarwa. Sai na tafi Kaduna Polytechnic inda na samu ƙwarewa da horaswa a kan koyar da aikin jinya da ungozoma. Bayan na gama sai aka tura ni sabuwar makaranta ta aikin ungozoma da ke Birnin Kudu a matsayin malama. Na yi aiki na wani lokaci daga nan sai na wuce ƙasar Indiya inda na samu digiri da Masters, wato BSc da MSc, a ɓangaren ‘Nursing’. Bayan na dawo sai na ci gaba da aiki a Birnin Kudu na wasu watanni, daga nan sai na samu aiki a tsangayar koyar da aikin jinya, wato ‘Department of Nursing Sciences’, a Jami’ar Bayero da ke Kano, inda har yanzu ina tare da su. A halin yanzu ina ƙasar Amurka inda na ke yin digiri na uku, wato PhD, duk dai a kan aikin jinyar.

Wasu na ganin zurfin ilimi ga ‘ya mace ba shi da amfani. Me za ki ce kan wannan?
Ina tsammanin masu ganin cewa ilimin ‘ya mace ba ya da amfani to ba su ma fahimci menene zaman duniya da tarbiyya ba. Kasancewar kaso mafi yawa na tarbiyyar ‘ya’ya ya na hannun mace, don haka ya na da matuƙar mahimmanci mace ta kasance mai ilimi. Idan uwa ta zama mai ilimi shi ne zai sa ta bada tarbiyya mai kyau kuma a samu nagartacciyar al’umma. Baya da tarbiyyar ‘ya mace idan ta samu ilimi za ta iya yin ayyuka da ya kamata ta yi a cikin al’umma kuma za ta taimaka wa ƙasar ta.

Menene matsayin sana’a ga ‘ya mace a wannan zamani?
Sana’a a
wannan zamani wajibi ne ga mace ko namiji. Idan mace ta na da sana’a ya na nufin za ta zama mai dogaro da kan ta, za ta iya kula da kan ta da ‘yan’uwan ta da kuma ‘ya’yan ta ko da ba ta da miji ko mijin ta ba ya da shi ko idan ma ba ya kula da ita.

A matsayin ki na mace, kin samu ƙalubale a tafiyar ki?
Ƙalubale da na samu na harkar karatu ne saboda barin ƙasa ta da kuma ‘yan’uwa na na tafi wata ƙasa don neman ilimi. Wannan ba ƙaramin ƙalubale ba ne a gare ni.

Nasarori fa?
Na samu nasarori da yawa, amma babbar nasarar da na samu ita ce kasancewa ta ɗaya daga cikin mata a Arewa masu zurfin ilimi da gogewa a ɓangaren aikin jinya. Na samu dama ta zuwa ƙasashen duniya daban-daban wanda wannan karatu nawa shi ya ba ni dama. Na yi nasarar yin abota da mutane manya masu ilimi a faxin duniya.

Ko Hajiya na tava siyasa?
Ban taɓa yin siyasa ba, kuma ba ni da sha’awar siyasa ko da nan gaba.

Ko menene dalilin ki?
E to, ina ga dalilin da ya sa ban son siyasa saboda ina son yin rayuwa ta watayawa ba tare da mutane sun san ni ba ko sun gane ni. Idan ka na siyasa duk motsin ka a idon mutane da ‘yan jaridu ya ke, ni kuma ba na son wannan. Dalili na biyu kuma shi ne ba na ƙaunar mulki ko kaɗan saboda abubuwan da ke cikin sa.

Wane irin kaya ki ka fi sha’awar sakawa?
Ina sha’awar duk wani kaya da zai suturta ni, saboda haka ina saka dogayen riguna na atamfa da abaya.

Ƙasashe nawa ki ka tava ziyarta?
Na ziyarci kasashe kusan ashirin.

Wace ƙasa ki ka fi so a cikin su?
Duk a cikin su na fi son ƙasar Indiya.

Wace kala ki ka fi so?
Ina son kalar ja.

Wane irin abinci ki ka fi so?
Ina matuqar son ɗanwake.

Menene bambancin abincin mu na Nijeriya da wasu ƙasashe?
(Dariya) Bambancin abincin mu da na sauran ƙasashe shi ne ina ga abincin mu ya fi ɗanɗano.

Ta yaya za a iya tallafa wa mata da ba su da ilimi ba sana’a?
Yadda za a taimaka wa mata da su ke zaune ba ilimi ba sana’a shi ne a ba su ilimi, domin ko da sana’a mutum zai yi ya na buƙatar ilimin wannan sana’a. Sa’annan su na buqatar a tallafa masu da jari wanda da shi ne za su samu damar dogaro da kan su.

Shin da gaske ne aure da wuri ne ke janyo matsalar yoyon fitsari?
Kamar yadda binciken masana ya nuna, auren wuri ba shi da wata dangantaka da lalurar yoyon fitsari. Macen da ta yi haihuwa da yawa ma ta na iya samu domin dalilin samuwar sa shi ne doguwar naƙuda, wato idan ya kasance mace ta na naquda ɗan bai fito ba to kan yaron ya kan matse mafitsara a jikin ƙashin ƙugu wanda wannnan matsewar ta kan hana jini gudana sai ta buɗe ta fara yoyo.

Wane kira za ki yi ga mazajen da ke ƙyama ko sakin matan su da su ka kamu da matsalar yoyon fitsari, alhali sun samu matsalar su na tare?
Kiran da zan yi wa maza masu ƙyama ko sakin mata saboda lalura ta yoyon fitsari shi ne su ji tsoron Allah. Wannan lalura (matan) sun same ta ne ta sanadin su mazan domin in ba don haihuwa ba zai yi wahala ta samu – duk da cewa akwai wasu abubuwa da su ke haddasa hakan amma ba su da tasiri kamar doguwar naƙudar – don haka mace ta na buƙatar kulawa ta ɓangaren jiki da ƙwaƙwalwa (physical and psychological). Hakan zai taimaka mata wajen samun sauƙi da kuma dawowa hayyacin ta saboda wannan matsala.

Menene babban burin ki a yanzu?
Babban buri na shi ne a ce na yi fice a kan ɓangaren ilimi na, yadda zan riƙa bada gudunmawa a duk duniya da za ta amfani al’uma baki ɗaya.

Menene muhimmancin ilimin ‘ya mace?
Ilimin ‘ya mace ya na da muhimmanci fiye da na namiji, domin idan ka ilmantar da namiji to shi ka ilmantar, yayin da in ka ilmantar da mace to kamar ka ilmantar da duniya ne. Ita tamkar makaranta ce mai zaman kan ta, inji Manzo Allah (SAW).

Mun gode da lokacin ki.
Ni ma na gode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *