‘Labarina’: Shirin fim ɗin Hausa mai dogon zango

Daga AYSHA SHAFI’EE a Kano

Shahararren mai bada umarnin nan Malam Aminu Saira tare da ƙwararren marubucin finafinan Hausa Ibrahim Birniwa, sun zo da wani sabon shiri na Hausa mai taken ‘Labarina’, wanda ake nunawa a tasha mai farin jini ta Arewa24, shiri ne mai dogon zango da ke ɗauke da fuskokin jaruman da mu ka sani da ma kuma wasu sababbin fuska.

Taurarin ciki sun haɗa da Nafisa Abdullahi a matsayin Sumayya, Nuhu Abdullahi a matsayin Mahmoud da kuma sabuwar fuska Maryam Isa Waziri a matsayin Laila. Sauran taurarin sun haxa da Hafsat Idris, Fatima Isa, Hadiza Muhammad, Ibrahim Bala, Ladi Tubeless, Isa Adam da kuma sauran su.

Labarina shiri ne da ke nuna rayuwar wata matashiya Sumayya, wadda ta tsinci kanta dumu-dumu cikin matsaloli a soyayya ta hanyar sadaukarwar da ba ta da amfani da kuma neman fata a inda babu shi.

Sumayya ta kasance ‘ya ɗaya a wajen mahaifiyar ta da su ke zaune a gidan haya, kwatsam sai mahaifiyar ta ta ta kamu da rashin lafiya har su ka dangana da asibiti inda a acan ne aka nemi da su siyo wasu magunguna.

Sumayya ta buga duk inda za ta samu tallafi ba ta samu ba don haka a qarshe sai ta yanke shawarar komawa wajen wani mai kyamis da ya nemi yin lalata da ita kafin ya taimaka mata da magungunan, inda anan ne ƙaddara ta haɗa ta wani saurayi Mahmud wanda ya ceto ta daga sharrin mai kyamis ɗin har ma kuma ya taimaka mata da kuɗin da ta sayi magungunan.

Wannan kyautatawa ta Mahmoud ta sa zuciyar Sumayya faxawa cikin son sa bayan shi ma ya furta mata hakan, kuma bayan soyayyar su ta fara ne sai su ka fara fuskantar ƙalubale daga vangarori da dama. Farko mahaifiyar Sumayya ta nuna ba ta son alaqar su amma bayan wani lokaci sai ta zo ta amince mata. Bayan soyayyar su ta fara ne sai Mahmud ya yi amfani da makauniyar soyayyar da Sumayya ke masa har ya raba ta da wani saurayin ta Lukman wanda ya zo da gaske don auren ta, duk kuwa da ƙoƙarin da ƙawar ta Rukkaya ta yi wajen ganin ta hana hakan.

Bayan rabuwar ta da Lukman ne sai Sumayya ta sake haɗuwa da wani saurayi mai suna Presido a makarantar su, Presido wani taƙadirin ɗan mai kuɗi da baya shakkar kowa. Ya nuna ya na son Sumayya ta hanyar takurawa da nuna isa, sai dai duk tarin matsawa da barazanar da ya dinga yi mata, Sumayya ba ta canja ra’ayin ta akan Mahmoud ba.

Amma duk wannan ƙoƙarin da ta yi akan sa sai ya tashi a banza bayan ya haɗu da wata yarinya mai suna Laila, Laila ‘yar gidan wani attajiri ce da ba ta jin fitar da kuɗi, wanda hakan ya ja Mahmud ga cin amanar Sumayya da kuma watsar da duk wata sadaukarwar ta a gare shi.

Abubuwan birgewa game da fim ɗin Labarina shi ne; tabbas shirin ya qayatu matuƙa wajen nishanɗantar da masu kallo ta hanyar sarƙaƙiyar da ta bayyana wani abu da ke yawan faruwa a rayuwar matasan yanzu. An yi ƙoƙari gaya wajen tsara zubin labarin, fitar da sautin sa, ɗaukar hoto da ma kuma tantance shi. Bugu da ƙari taurarin sun yi bajinta wajen fito da taswirar labarin tsaf. Jaruma Nafisa Abdullahi ta taka rawa wajen fito da halayyar Sumayya tamkar a gaske, Nuhu Abdullahi ya dace da saurayi Mahmoud yayin da Fatima Isa ta karvi matsayin ta na Rukkaya. Sauran taurarin har ma da sababbin fuskar da aka nuna duka sun dace da matsayin su ta yadda su ka fito da zaren labarin tamkar a gaske.

Sai dai duk yadda labarin ya kai ga tafiya kuma masu kallo ke jiran cigaban zango na uku, za’a iya cewa shirin ya fi karkata ne ga samun ra’ayoyi da kuma motsa zukatan masu kallo fiye da bayyana wata ma’ana guda ɗaya ƙwaƙƙwara, a taƙaice dai shirin ba shi da wata cikakkiyar ma’ana ko wani saƙo da aka isar wa masu kallo, musamman ma a ƙarshen zango na biyu inda aka yi gaggawa wajen ƙarƙare Labarin da wasu gutsirarrun bayanai. Hakazalika suturun da Laila ke sanyawa a cikin shirin ba su dace sosai da matsayin ta na mai kuɗi da aka nuna ba.

Amma duk da wannan ‘yar tangarɗar, za mu iya cewa Labarina shiri ne da kowa zai ji daɗin kallon sa musamman ma matasa, hakazalika shiri ne da zai ƙara ƙaimi ga masoyan Malam Aminu Saira.

08067794315
[email protected]