Siyasa

Gwamnonin Kudu sun haramta kiwo barkatai a yankinsu, sun buƙaci a sake fasalin ƙasa

Gwamnonin Kudu sun haramta kiwo barkatai a yankinsu, sun buƙaci a sake fasalin ƙasa

Yayin wani taro da suka gudanar a ranar Talata a Asaba babban birnin jihar Delta, gwamnonin Kudu sun yi ittifaƙi kan haramta kiwo barkatai a yankinsu. Cim ma wannan matsaya da gwamnonin suka yi hakan ba ya rasa nasaba da matsalar tsaron da suka ce yankin nasu na fama da ita. Kazalika, yayin taron nasu gwamnonin sun ƙalubalanci Gwamnatin Tarayya a kan ta gaggauta sake fasalin ƙasa domin magance matsalolin tsaron da ke ci gaba da cinye wa ƙasa tuwo a ƙwarya.
Read More
Arewa ta Tsakiya na kwaɗayin shugabancin APC na ƙasa

Arewa ta Tsakiya na kwaɗayin shugabancin APC na ƙasa

Daga BASHIR ISAH Yankin Arewa ta tsakiya ya nuna ƙudirinsa na neman shugabancin jam'iyyar APC a matakin ƙasa. Yankin ya bayyana sha'awarsa kan neman shugabancin jam'iyyar ne sa'ilin da masu ruwa da tsaki na Jam'iyyar a yankin suka ziyarci Gwamnan Neja kuma Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa ta Tsakiya, Abubakar Sani Bello, s fadar gwamnatin jihar da Minna, babban birnin jihar. Yayin da yake bayani kan irin gwagwarmayar da yankin ya sha dangane da yi wa APC hidima tun bayan kafiwarta, Gwamna Sani ya ce bai kamata a baro yankin a baya ba. Yana mai cewa sun amince su shiga a…
Read More
‘Yan takarar ciyaman 38 sun faɗi gwajin auna fahimta a Kaduna

‘Yan takarar ciyaman 38 sun faɗi gwajin auna fahimta a Kaduna

Daga UMAR M. GOMBE Jam'iyyar APC ta jihar Kaduna ta bayyana rashin cancantar tsayawa takara na wasu mutum 38 daga cikin mutum 115 da suka nuna sha'awarsu ta tsayawa takarar shugabancin ƙananan hukumomin jihar. Uwar jam'iyyar APC ta jihar ta ce, waɗanda lamarin ya shafa an same su da dalilan da suka hana canantarsu shiga takara kama daga dalili na mutum na da wani tabo na laifi da ya taɓa aikatawa ko kuma ya faɗi a gwajin auna fahimtar da aka ba su su rubuta. Manhaja ta kalato cewa wannan shi ne karo na farko a tarihin Nijeriya da aka…
Read More
Za mu tsige Buhari muddin magance matsalar tsaro ya faskara – Hon Bagos

Za mu tsige Buhari muddin magance matsalar tsaro ya faskara – Hon Bagos

Daga AISHA ASAS Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar shiyyar Jos ta Kudu da Jos ta Gabas a Majisar Wakilai ta Ƙasa, Dachung Bagos, ya ce majalisa za ta ɗauki matakin tsige Shugaba Muhammadu Buhari muddin Majalisar Zartarwa ta Kasa ta kasa kawo ƙarshen matsalolin tsaron da suka addabi ƙasa. Ɗan majalisar ya yi wannan furuci ne yayin wani shiri da aka yi da shi a wannan Alhamis ɗin a tashar talabijin ta Channels. Idan dai za a iya tunawa, ko Larabar da ta gabata sai da majalisar ta kafa wani kwamiti na mutum 40 tare da ɗora masa aikin binciko…
Read More
Sanata Ordia ya tsallake rijiya da baya sau biyu a yini guda

Sanata Ordia ya tsallake rijiya da baya sau biyu a yini guda

Daga FATUHU MUSTAPHA Har sau biyu 'yan bindiga na kai wa Sanata Clifford Ordia (PDP Edo ta Tsakiya) hari a Litinin da ta gabata a hanyar Okenne zuwa Lokoja da kuma hanyar Lokoja zuwa Abaji. Sanata Ordia wanda shi ne shugaban kwamitin Majalisar Dattawa kan Basussukan Cikin Gida da Waje, ya yi wa manema labarai bayanin yadda ya kuɓuta daga harin 'yan bindigar da suka buɗe wa tawagar motocinsa wuta a kan hanyarsa ta komawa Abuja daga jihar Edo. Ya ce sakamakon musayar wuta da aka yi tsakanin jami'an tsaron da ke ba shi kariya da ɓarayin, wasu 'yan sanda…
Read More
Zaɓen Ondo: Kotu ta yi watsi da ƙarar da PDP ta shigar

Zaɓen Ondo: Kotu ta yi watsi da ƙarar da PDP ta shigar

Kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ta jihar Ondo, ta yi watsi da ƙarar da jam'iyyar PDP ta jihar da ɗan takararta Eyitayo Jegede, suka shigar inda suke ƙalubalantar nasarar da Gwamna Oluwarotimi Akeredolu SAN na APC ya samu a zaɓen gwamnan jihar da ya gudana ranar 10 ga Oktoban 2020. Kotu ta kori ƙarar ne saboda rashin ƙarfin iko da cancanta. Da yake gabatar da shari'ar ta bidiyo, shugaban kotun, Alƙali Umar Abubakar, ya ce batun da aka shigar da ƙara a kansa abu ne da jam'iyyar za ta sasanta ta cikin gida ba tare an kai kotu ba, wanda a…
Read More
Hukumar Zaɓe za ta hukunta jam’iyyu masu yin rikici a babban taron su

Hukumar Zaɓe za ta hukunta jam’iyyu masu yin rikici a babban taron su

Daga WAKILINMU Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta yi barazanar za ta hukunta duk wata jam'iyyar siyasa wadda ta kasa gudanar da babban taron ta (congress) cikin lumana. A cikin wata sanarwa da ta bayar a ranar Litinin, INEC ta ce akwai yiwuwar ba za ta amince da sakamakon da aka samar a babban taron jam'iyyar da aka yi a cikin hatsaniya ba idan har ba a daina wannan ɗabi'ar ba. Kakakin hukumar, Mista Festus Okoye, ya ce ƙazancewar rikicin da ake samu a wajen babban taron jam'iyya ya na sanyawa hukumar ta samu “matuƙar wahala” wajen gudanar da aikin…
Read More
Zaɓen 2023 da kamar wuya muddin ba a magance matsalar tsaro ba – Ejiofor

Zaɓen 2023 da kamar wuya muddin ba a magance matsalar tsaro ba – Ejiofor

Daga UMAR M. GOMBE Tsohon Daraktan Sashen Tsaron DSS, Mike Ejiofor, ya ce duba da yadda fannin tsaron ƙasar nan ke ta sukurkucewa ya sa yake ganin da kamar wuya a iya gudanar da zaɓuɓɓukan 2023. Ejiofor ya yi wannan bayani ne yayin hirar da aka yi da shi a tashar Channels a ranar Litinin. Ya ce tun dare bai yi mata ba ya kamata Gwamnatin Tarayya ta gaggauta ɗaukar matakin daƙile wannan matsalar da ta yi wa ƙasa tarnaƙi. Yana mai cewa, “Muddin ba a magnace matsalar tsaron da ta addabi sassan ƙasa kafin zaɓuɓɓukan 2023 ba, ina mai…
Read More
Ba mu yarda da ci gaban shugabanci mara kan gado ba – PDP

Ba mu yarda da ci gaban shugabanci mara kan gado ba – PDP

Daga AISHA ASAS Babbar jam'iyyar bamayya a Nijeriya, PDP, ta ce duk da dai tana yi wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari barka da dawowa daga jinyar da ya je a Turai, amma ba ta yi na'am da zancen shugaban ba na cewa 'yan Nijeriya su sa ran ganin "Ci gaba." A bayanin da ta fitar, PDP ta ce tana ra'ayin ko ma dai da wata manufa shugaban ya furta kalmar 'Ci gaba' ɗin, kada hakan ya yi nasaba da barin mulkinsa ya zuwa 29, Mayu, 2023. Ta ci gaba da cewa hasali ma 'yan Nijeriya ba su yarda da duk…
Read More
Cross River: Shirin sauya sheƙar Gwamna Ayade ya kaɗa hanjin PDP

Cross River: Shirin sauya sheƙar Gwamna Ayade ya kaɗa hanjin PDP

Daga UMAR M. GOMBE Domin gudun kada ta rasa ɗanta, Jam'iyyar PDP ta tura a rarrashi Gwamnan Jihar Cross River, Ben Ayade,bayan da ta gano cewa gwamnan na shirin sauya sheƙa zuwa APC. Binciken Manhaja ya gano cewa matakin sauya sheƙar da Gwamna Ayade ya ɗauka ba ya rasa nasaba da rasa ƙarfin ikon jan akalar PDP a jihar ga 'yan majalisar ƙasa daga jihar kamar yadda ya bayyana yayin wani taro da suka gudanar kwannan nan. Haka nan, Manhaja ta tattaro cewa ɗaukacin shugabannin ƙananan hukumomin jihar su 18 da kansilo196 ba su saɓa wa umarnin gwamnan saboda cikakkiyar…
Read More