Hukumar Zaɓe za ta hukunta jam’iyyu masu yin rikici a babban taron su

Daga WAKILINMU

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta yi barazanar za ta hukunta duk wata jam’iyyar siyasa wadda ta kasa gudanar da babban taron ta (congress) cikin lumana.

A cikin wata sanarwa da ta bayar a ranar Litinin, INEC ta ce akwai yiwuwar ba za ta amince da sakamakon da aka samar a babban taron jam’iyyar da aka yi a cikin hatsaniya ba idan har ba a daina wannan ɗabi’ar ba.

Kakakin hukumar, Mista Festus Okoye, ya ce ƙazancewar rikicin da ake samu a wajen babban taron jam’iyya ya na sanyawa hukumar ta samu “matuƙar wahala” wajen gudanar da aikin da ya rataya a wuyan ta na kula da jam’iyyun.

Ya ƙara da cewa ana lalata kayan hukumar a ƙarshe a yayin da kuma rayukan masu shiga taron da na jami’an hukumar ke fuskantar barazana.

Okoye ya ce, “Wannan hukumar ba za ta zura ido ta na kallon yadda ababen takaici da rikice-rikice ke aukuwa a manyan tarurrukan jam’iyyu ba, inda kuma ake barazana ga rayuka tare da ɓarnata kayayyaki.

“Shakka babu, daga yanzu INEC za ta sake duba rawar da ta ke takawa a waɗannan abubuwan, idan har su ka ci gaba da jefa rayuwar jama’a da ma’aikatan hukumar cikin haɗari.

“Saboda haka, za a gamu da fushin hukuma sosai a duk lokacin da babban taron jam’iyya ya zama na tada husuma da lalata kayayyakin INEC. Ban da sake mayar da irin waɗannan kayayyakin da aka ɓarnata, akwai yiwuwar a soke jam’iyyun daga karɓar kayan INEC don gudanar da ayyukan su a nan gaba.

“Haka kuma mai yiwuwa ne hukumar ta janye ma’aikatan ta daga sa ido kan irin waɗannan tarurrukan na tada husuma da jam’iyyun ke yi, wanda hakan zai haifar da ƙin amincewa da jam’iyyar ma kwata-kwata.”

Hukumar ta tunatar da jam’iyyun siyasa cewa akwai zaɓuɓɓukan share fage da ke tafe inda za su zaɓi ‘yan takarar su na zaɓuɓɓukan da za a yi da zaɓuɓɓukan cike gurbi, musamman zaɓen gwamnan Jihar Anambra da zaɓuɓɓukan ƙananan hukumomin Gundumar Babban Birnin Tarayya (FCT).

Okoye ya ce, “Tilas ne jam’iyyu su tsaya su yi aiki da jadawalin lokutan da aka fitar na abubuwan da za a yi a waɗannan zaɓuɓɓukan kamar yadda hukumar ta fitar da shi, wanda kuma an aika masu shi kuma akwai shi a gidan yanar INEC (www.inec.gov.ng).

“Tilas ne jam’iyyun su tabbatar da cewa zaɓuɓɓukan su na fidda gwani an yi su cikin lumana da kyakkyawan tsari.

“Abu mafi muhimmanci shi ne tilas su bi Dokar Zaɓe sau da ƙafa, da Dokoki da Tsare-tsaren INEC, da kuma kundayen tsarin mulki da ƙa’idojin jam’iyyun, waɗanda hukumar ta na da su a hannun ta.

“A ƙarshe, a wajen gudanar da ayyukan su na cikin gida, tilas ne jam’iyyun siyasa su ɗauki kan su da daraja kamar yadda su ka ɗauki hukumar a lokacin zaɓuɓɓuka, wato su yi komai a bayyane, da tsare gaskiya, da bin dokoki da yin komai cikin lumana.

“INEC na ci gaba da damuwa sosai kan hatsaniya da tada hankali a cikin jam’iyyu ta yadda a yanzu akwai ƙararraki a kotuna daban-daban waɗanda aka shigar a dalilin manyan tarurruka da zaɓuɓɓukan share fage da hukumar ta gudanar.

“Duk da haka, hukumar za ta ci gaba da yin aiki da goyon bayan jam’iyyun siyasa wajen tallafa wa ayyukan su na cikin gida domin a gina tsarin dimokiraɗiyya mai nagarta a Nijeriya.”

Kwanan nan ne dai rikice-rikice su ka ɓarke a wajen manyan tarurruka da wasu jam’iyyu su ka gudanar, musamman ma dai jam’iyyar PDP.