Maniyyatan Pakistan 50,000 ne za su sauke farali bana

Daga AISHA ASAS

Kimanin maniyyata 40,000 zuwa 50,000 daga ƙasar Pakistan ake sa ran za su yi aikin Hajjin bana, in ji Ministan Harkokin Addini na Ƙasar, Sahibzada Noor-ur-Haq Qadri.

Ministan ya bayyana haka ne a Lahadin da ta gabata, tare da cewa hajjin bana zai gudana ne ƙarƙashin kulawa ta musamman saɓanin yadda aka saba gani a baya, inda aka gindaya dokoki da sharuɗɗa na musamman.

Ya ce ana buƙatar maniyyatan su bi ƙa’idojin da aka shimfiɗa sau da ƙafa yayin aikin hajjin. Ya ci gaba da cewa, maniyyatan da aka tabbatar sun yi allurar rigakafin korona kaɗai za a bai wa damar gudanar da aikin hajjin bana.

A cewar Minista Qadri ma’aikatarsa a shirye take tsaf ta bi umarni tare da kiyaye duka dokokin da aka shimfiɗa don aikin hajjin 2021.

Ya ce mai yiwuwa maniyyata ‘yan ƙasa da shekara 20 da kuma ‘yan sama da shekara 50 ba za su samu damar yin Hajjin bana ba.

A cewarsa, mutanen da ba su da matsalar rashin lafiya Saudiyya za ta sahale wa aikin hajjin.

Sai dai ya ce har yanzu babu wata alama da Gwamnatin Saudiyya ta bayar kan ci gaba da shirye-shiryen hajjin, amma cewa sassa daban-daban na hukumomin Saudiyya na ci gaba da nazari kan yadda za a samu halin gudanar da hajji mai cikakken kariya da kuma sukuni.
.