Mutum biyu sun rasu a haɗarin hanyar Kaduna

An yi fargabar wasu mutum biyu sun mutu sakamakon wani mummunan haɗarin da ya faru a yankin Jere kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja a wannam Litinin.

Bayanan da Manhaja ta tattara sun nuna motoci biyun da haɗarin ya rutsa da su sun baro Abuja zuwa Kano ne inda akasin ya auku.

Ya zuwa haɗa wannan labari, ba a bayyana dalilin aukuwar haɗarin ba.

Tuni dai labarin aukuwar haɗarin ya isa ofishin jami’an kiyaye haɗurran kan haya mafi kusa.